@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
YAHUDU SUN SAN SHI FIYE DA YADDA SUKA SAN 'YA'YANSU
Ayoyin Alqur'ani sun zo da busharar zuwansa (S. A. W. W) wanda Annabawa /Manzanni (A. S.) su kayi bayaninsa cikin al'ummunsu.
Zuwansa babbar rahma ce gare mu, kuma dukkan Manzanni (A. S) da suka gabace shi sun zo ne a matsayin 'yan sharar fage na zuwansa .
Babu wani Manzo da bai yi busharar zuwansa ga al'ummasa ba, saboda haka ne ma Yahudu suka san shi fiye da yadda suka san 'ya'yansu.
Allah (T) ya tabbatar mana da hakan cikin littafinsa mai tsarki cewa Yahudu sun san Shi fiye da yadda suka san 'ya'yansu .
DAGA TAFSIRIL-QUMMIY
Sheikh Abbas Al-Qummiy ya kawo cikin tafsirinsa kamar haka,
فس، تفسير القمي الَّذِينَ آتَيْناهُمُ الْكِتابَ يَعْرِفُونَهُ كَما يَعْرِفُونَ أَبْناءَهُمُ الْآيَةَ فَإِنَّ عُمَرَ بْنَ الْخَطَّابِ قَالَ لِعَبْدِ اللَّهِ بْنِ سَلَامٍ هَلْ تَعْرِفُونَ مُحَمَّداً فِي كِتَابِكُمْ قَالَ نَعَمْ وَ اللَّهِ نَعْرِفُهُ بِالنَّعْتِ الَّذِي نَعَتَهُ اللَّهُ لَنَا إِذَا رَأَيْنَاهُ فِيكُمْ كَمَا يَعْرِفُ أَحَدُنَا ابْنَهُ إِذَا رَآهُ مَعَ الْغِلْمَانِ وَ الَّذِي يَحْلِفُ بِهِ ابْنُ سَلَامٍ لَأَنَا بِمُحَمَّدٍ هَذَا أَشَدُّ مَعْرِفَةً مِنِّي بِابْنِي قَالَ اللَّهُ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنْفُسَهُمْ فَهُمْ لا يُؤْمِنُونَ[20]
" Lalle wadanda aka bawa littafi sun san shi (S. A. W. W) kamar yadda suka san 'ya'yansu (AYA) ." Domin Umar Bn Khaddab ya tambayi Abdullahi Bn Salam ;
" Shin, kun san Muhammadu cikin littafinku ? (Abdullahi Bn Salam) yace,
" EH, WALLAHI MUN SAN SHI NE TA HANYAR SIFFANTAWAR DA ALLAH YA SIFFANTA MANA SHI, MUNA GANE SHI CIKINKU KAMAR YADDA 'DAYAN MU KE IYA GANE 'DANSA YAYIN DA YAKE TARE DA JARIRAI . NA RANTSE DA ABINDA IBN SALAM KE YIN RANTSUWA DA SHI, SHI WANNAN MUHAMMADUN NA FI TSANANIN SANINSA FIYE DA YADDA NA SAN 'DANA. "
Allah na cewa,
" LALLE WADANDA SU KAYI HASARA (ta hanyar bijire masa bayan sun gan shi kuma sun gane shi kamar yadda aka siffanta musu shi ), TO, BA ZA SU TABA YIN IMANI BA. "
(2) تفسير القمّيّ: 182
To, kamar yadda Yahudu su kayi hasara ta hanyar bijirewa Annabi (S. A. W. W), hakane ma da wannan al'ummah tayi hasara sakamakon bijirewa Sayyid Zakzaky (H) alhali sun san busharar da 'Dan Fodiyo yayi a kansa, kuma sun gane cewa shine wannan Mujaddadi wanda zai jaddada addinin kakansa (S. A.W.W).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08138925034
18th October, 2020/ 1st Rabi'ul-Awwal, 1442.