Burin Dukkan Namiji Ya Tara Mata da Dukiya !!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KABI ALLAH DA TAQWA KAWAI KA SAMI ABINDA YA FISU ALKHAIRI 


'Dabi'a ce wacce Allah ya halicci dan Adam da ita na yawan sha'awace-sha'awacen abubuwa da dama , shi yasa kaga 95% na mutane sun nutse cikin sha'awar mata, 'ya'ya da kuma dukiya. 


Ba abin zargi bane don mutum na sha'awar wadannan abubuwa kuma ya neme su ta kyakkyawar hanya. 


Allah (T) na fada cikin Alqur'ani cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ ٱلشَّهَوَٰتِ مِنَ ٱلنِّسَآءِ وَٱلۡبَنِينَ وَٱلۡقَنَٰطِيرِ ٱلۡمُقَنطَرَةِ مِنَ ٱلذَّهَبِ وَٱلۡفِضَّةِ وَٱلۡخَيۡلِ ٱلۡمُسَوَّمَةِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ وَٱلۡحَرۡثِۗ ذَٰلِكَ مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلۡمَـَٔابِ ٤١


" AN QAWATAWA MUTANE SON SHA'AWOWI DAGA MATA DA 'YA'YA DA DUKIYOYI ABABEN TARAWA DAGA ZINARIYA DA AZURFA, DA DAWAKI KIWATATTU (Jeep-Jeep da Daf-Daf a wannan zamani ) DA DABBOBI (na ci) DA KUMA AMFANI GONA. WADANNAN (duk) JIN DADI NE NA RAYUWAR DUNIYA , KUMA ALLAH A WAJENSA KYAKKYAWAR MAKOMA TAKE. "


Su kuwa wadannan abubuwa a cikinsu ake halaka duk da cewa nemansu halas ne gare mu, sai dai da yawa mutane na shagala cikinsu kuma su gafala da neman abinda shi ba jin dadi na rayuwar duniya bane. 


Saboda haka Allah (T) ya ankarar damu don kada mu gafala yake cewa Manzo (S. A.W.W)


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 ۞قُلۡ أَؤُنَبِّئُكُم بِخَيۡرٖ مِّن ذَٰلِكُمۡۖ لِلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَأَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞ وَرِضۡوَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ ٥١


" KACE; SHIN KUMA NA BA KU LABARI GAME DA ABINDA YAFI ALKHAURI DAGA WANNAN (wanda aka lissafo muku a sama) ?


AKWAI GIDAJEN ALJANNAH A WAJEN UBANGIJI (wanda ya tanade su kawai ) SABODA WADANDA SUKA BI SHI DA TAQAWA, KOGUNA SUNA GUDANA DAGA QARQASHINSU, SUNA MADAWWAMA A CIKINSU. DA KUMA MATAN AURE (nasu) TSARKAKAKKU (wadanda ba sa haila ko biqi), DA KUMA YARDA DAGA ALLAH (wanda shi yafi komai dadi). KUMA ALLAH MAI GANI NE GA BAYINSA (cikin dukkan wani motsi nasu) ."


(Al-Imran, aya ta ta 14-15)


NB :- Abin lura anan shine, wallahi duk wanda ya shagaltuwa cikin abubuwan da aka lissafo cikin aya ta 14, to, ba zai sami abinda aka ambato su cikin aya ta 15 ba, domin Allah ya ambaci dukiya da 'ya'ya a matsayin fitina ce gare mu, kuma fitina ba kowa ke iya fitar da kansa daga cikinta ba . 


Allah ya amfanar damu daga wannan tunatarwar.

 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

       (08126385470)


19th October, 2020/ 2nd Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post