@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN KA AMSA KIRANSU WUTA ZA SU KAIKA
Wani lokaci nakan rasa dalilin da yasa wasu jama'ah ke qoqarin danqarawa mutane yin koyi da wasu ko wata qasa wajen ayyukan addininsu. Jahilci ne ke sa su yin haka ko kuma dai bin son zuciya , nakan kasa tantance gaskiyar maganar .
Allah (T) bai umarce da muyi koyi da Annabi (S. A. W. W) don shi Balarabe bane, a'a, domin shi dan saqo ne daga gare shi kamar yadda sauran 'yan saqo suka kasance gabaninsa.
Ya zo cikin wata riwaya daga Huzaifatul-Yamani inda ya kawo abinda Annabi (S. A. W. W) yayi masa nuni da kuma gargadi don yasan irin wadanda zai yi riqo ko koyi dasu.
Ga riwayar nan kamar haka;
2994 - 1371 - «تكون دعاة على أبواب جهنم من أجابهم إليها قذفوه فيها هم قوم من جلدتنا يتكلمون بألسنتنا فالزم جماعة المسلمين وإمامهم فإن لم تكن جماعة ولا إمام فاعتزل تلك الفرق كلها ولو أن تعض بأصل شجرة حتى يدركك الموت وأنت كذلك» .
(صحيح) ... [هـ] عن حذيفة. خ - فتن، م - إمارة.
FASSARA
------------------
" KIRAYE-KIRAYE (masu yawa) ZA SU KASANCE A QOFAR JAHANNAMA , WANDA YA AMSA MUSU ZA SU JEFA SHI CIKINTA.
SU WASU JAMA'AH NE DAGA FATARMU (fararen fata larabawa), KUMA SUNA MAGANA DA HARSHENMU (larabci) . TO, KA LAZIMCI JAMA'AR MUSULMI DA LIMAMINSU.
IDAN KUWA YA KASANCE BABU JAMA'AH KUMA BABU LIMAMI , TO, KA NISANCI DUKKAN WADANNAN RABE-RABE GABA 'DAYANSU KO DA KUWA ZA KA TA'ALLAQA NE DA JIKIN BISHIYA HAR MUTUWA TAZO MAKA KANA HAKA (cikin wannan matsayi) ."
Wannan magana mun tsamota ne daga (SAHIHU JAAMI'US-SAGEER ).
SHARHI
Abinda wannan hadisi ke nuna mana shine, kiraye-kiraye za su kasance masu yawa, kuma ko wacce murya tana nuni ne cewa akan gaskiya take, kuma burinta shine a amsa mata.
Ma'aunin gane jama'ah mai limami shine kaga jama'ah masu yawa amma suna da shugaba qwaya daya (1) tal wanda kowa ke yarda da ma'anarsa, masu bada rai don fansar ransa, masu sallamar da komai nasu na daga dukiya ko ilimi ko lokaci wajen bashi kariya da taimakonsa, ko da kuwa akwai sabani cikin wadannan mabiya nasa.
Duk jama'ar da basu da shugaba wanda suke ji da kuma dauka daga gare shi, sannan suna iya yi masa tawaye saboda maganganunsa masu cin karo da juna ko kuma saboda miqa wuyansa ga azzalumai da zumunci, to, wadannan ba sune jama'ar da ake so a kasance cikinsu ba, domin sune masu kira zuwa wuta !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08126385470-08137925034)
1st October, 2020/ 14th Safar, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com