@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Sanin qima shine mutum ya dauke ka a matsayin mutum mai daraja, mai kamala mai mutunci kamar yadda yake ganin kansa.
Akwai wasu nau'in mutane wadanda duk wata mu'amalar da za suyi da kai sukan dauke ka wani qasqantacce ne a wajensu, ma'ana ba sa ganin kamar ka kaisu ko ma ace ka fi su.
To, su irin wadannan mutane ko a tafiya ne babu amfanin yi tare dasu sai dai bisa lalura. Mutumin da yake ganin kamar ka fi shi ko da kuwa ba kama kaishin ba shine abokin tafiya, domin akwai mutunta juna.
Ya zo cikin wani hadisi daga Imam Ali (A. S) cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وَ بِإِسْنَادِهِ قَالَ قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع لَا تَصْحَبَنَّ فِي سَفَرٍ مَنْ لَا يَرَى لَكَ الْفَضْلَ عَلَيْهِ كَمَا تَرَى لَهُ الْفَضْلَ عَلَيْكَ[10].
" KADA KAYI ABOTA CIKIN TAFIYA TARE DA WANDA BA YA GANIN FIFIKONKA A KANSA KAMAR YADDA KAKE GANIN FIFIKONSA A KANKA ."
Idan ya kasance kowa na ganin fifikon dan'uwansa a kansa to, za afi samun nutsuwa tare da mutunta juna. Amma in aka sami akasin haka tafiyar za ta zama ana yinta ne kawai babu aminci da girmamawa.
Na'am, ta bangarensa ba shi da matsala matuqar kai kana ganin fifikonsa a kanka, amma ta naka janibin akwai matsala in har shi ba ya ganin fifikonka a kansa.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج73، ص: 268
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034-08126385470)
9th October, 2020/ 22nd Safar, 1442.