Ba Kai Suke Qaryatawa Ba Yaa Sayyid, Da Ayoyin Allah Suke Jayayya !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SUNNAR ALLAH CE WACCE BA TA CANZAWA 


Idan ka nazarci halayyar shugabannin wannan qasa Nigeria da kuma jagororin masu da'awa ta muslimci sai abin ya baka mamaki, domin gaba dayansu sun juya akalarsu ce zuwa ga duniya da neman dawwama a cikinta. 


Umarnin Allah ne cewa mu riqe littafinSa Alqur'ani a Matsayin jagora wanda zai jagorance mu cikin rayuwarmu ta duniya da lahira, kowa ya san haka kuma an san ba shine ke Jagorantar rayuwarmu ba. 


Cikin irin wannan yanayi aka sami mai kira zuwa ga wannan littafi don ya zama mai yin hukunci a tsakaninmu, amma maimakon a amsa masa sai ya zamana ana yin munanan maganganu a kansa da kuma fassara shi a matsayin dan ta'adda, da kuma cutar da shi ta kowacce fuska. 


Shi kuwa wannan bawan Allah bai fasa wannan kira nasa ba, su ma basu fada yi masa sharruka da cutarwa ba. 


Lalle Allah na tare dashi kuma yana qarfafarsa kan wannan jan aiki da ya runguma. Shine yake rarrashinsa da cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



قَدۡ نَعۡلَمُ إِنَّهُۥ لَيَحۡزُنُكَ ٱلَّذِي يَقُولُونَۖ فَإِنَّهُمۡ لَا يُكَذِّبُونَكَ وَلَٰكِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ يَجۡحَدُونَ ٣٣ 


" HAQIQA MUNA SANI LALLE SHI ABINDA SUKE FADA ( na cutarwa da muzantawa gare ka ) YANA 'BATA MAKA RAI , TO, LALLE SU BA QARYATAKA SUKE YI (cikin zukatansu kan ba akan gaskiya kake ba), SAI DAI SU AZZALUMAI SUNA JAYAYYANE DA AYOYIN ALLAH (don bin son zuciyarsu) ."


Saboda haka wannan abu ba farau bane kuma ba qarau bane, domin haka sunnar Allah take. Duk wanda ya tashi yana kira na gaskiya sai azzalumai da miyagun malamai sunyi masa taron dangi. 


Shine Allah (T) yake sanar dashi cewa; 


وَلَقَدۡ كُذِّبَتۡ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِكَ فَصَبَرُواْ عَلَىٰ مَا كُذِّبُواْ وَأُوذُواْ حَتَّىٰٓ أَتَىٰهُمۡ نَصۡرُنَاۚ وَلَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِ ٱللَّهِۚ وَلَقَدۡ جَآءَكَ مِن نَّبَإِيْ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ٤٣ 


 " KUMA HAQIQA (irin su) SUN QARYATA MANZANNI (masu yawa) GABANINKA, AMMA SAI SUKA YI HAQURI AKAN WANNAN QARYATAWAR, KUMA AKA CUTAR DASU HAR TAIMAKONMU YAZO MUSU . BABU MAI CANZA KALMAR ALLAH (komai cigaban zamani hanyar kenan). KUMA HAQIQA (irin wannan cutarwa da bata suna) YA ZO MAKA DAGA LABARIN MANZANNI (da suka shude) ."


(AN'AM, AYA TA 33-34)


Mu kuma a matsayinmu na mabiyansa (H) dole mu lura da wannan don shi zai qara mana yaqini cewa muna bayan wanda ya gaji Annabawa kuma Manzanni (A. S). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda.


(08126385470-08137925034)


17th October, 2020/ 30th Safar, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post