Ashe Har A Bayan Wafatin Annabi (S.A.W.W) Ana Gane Munafukai !!!


 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SON ALI MA'AUNI NA GANE MUMINI 

Na gani cikin wani hadisi wanda aka riwaito daga Umar Bn Khaddab cikin Riyadus-Saaliheen inda yake cewa a zamanin Annabi (S. A. W. W) akan saukar da aya ce wacce take nuna musu munafukan cikinsu qarara, amma bayan wafatinsa (S. A. W. W) basa iya gane munafuki, sai dai kawai sukan hukunta mutum ne da zahirinsa. 

Amma dana qara nutsewa cikin wani littafi mai suna MUSNAD-NISAA'I sai naci karo da wani hadisi kamar haka; 

25909- حَدَّثَنَا عُثْمَانُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ أَبِي شَيْبَةَ , قال عبد الله : وَسَمِعْتُهُ أَنَا مِنْ عُثْمَانَ بْنِ مُحَمَّدٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ فُضَيْلٍ ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ أَبِي نَصْرٍ ، قَالَ : حَدَّثَنِي مُسَاوِرٌ الْحِمْيَرِيُّ ، عَنْ أُمِّهِ ، قَالَتْ : سَمِعْتُ أُمَّ سَلَمَة َ , تَقُولُ : سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ لِعَلِيٍّ : " لَا يُبْغِضُكَ مُؤْمِنٌ ، وَلَا يُحِبُّكَ مُنَافِقٌ " .

Usman Bn Muhammad Bn Shaibata ya bamu labari, Abdullahi yace; Ni na ji shi daga Usman Bn Muhammad yace, Muhammad Bn Fudhail ya bamu labari daga Abdullahi Bn Abdurrahman baban Nadhari yace, Misaawiru Al-Himyariyyu ya bani labari daga mamarsa tace; 

Naji Ummus-Salamata na cewa; Naji Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa Aliyu, 

" MUMINI BA YA QINKA, KUMA MUNAFUKI BA YA SONKA !"

(MUSNAD-NASAA'I) 

Tun daga lokacin dana karanta wannan hadisi nasan cewa ashe har yanzu ma a wannan zamani ana gane munafukai ta hanyar nuna qiyayyarsu ga Imam Ali (A. S). 

To, ina kuma ga wadanda suka hana masa haqqinsa ko kuma suka yaqe shi da zuriyarsa (A. S) ?

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

        0812638540


3rd October, 2020/ 16th Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post