AREWA:-'MaiMakon 'Yan Arewa Su yabeta, Wasu Har Zangin ta Sukeyi !!!

 


Maimakon su kalli Hijabin Malama Aisha su yabeta akai, ko kuma su yabeta saboda jarumtarta da dakewa. Amma sai suka shagala da zaginta ba tareda tayi laifin komai ba. Kwarai! Nace batayi laifi ba, idan kuma tayi laifin wa tayiwa? Allah? Ko kai? Idan kace mun tayi laifi a ganinka, to wanene kai din? Mahaliccinta? Mahaifanta? Ko Mijinta?

Kayi zaton cewa sai kowa ya rayu bisa irin tunaninka jahilcine da wauta. Haka mafi yawan mutanenmu suke, wasuma sun dauka hatta Allah baya kar6an aiki sai wanda ya dace da ra'ayinsu. Wannan tasa da zarar ka sa6a musu zasu yanke maka hukumci.

Yanzu dai kowa ya gane cewa kunne "Baba" Danliti ya warke, duk da cewa ya dena jin Hausa, amma Alhamdulillah yana jin irin yaren su Malama Aisha.

-Ahmad Bawa Jalal

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post