Anya ba za mu yi tunani cewa akwai abin da ya faru a farkon watan Mauludi wanda yana iya kaiwa ga wani al'amari ba?
Anya muna tsammanin cewa shekar da jinanan yan'uwanmu da azzalumai suka yi ba zai zama asasin tunbuke zaluncin azzaluman nan ba kuwa?
Anya muna gasgata sadaukarwar wadannan jaruman tsayayyun bayin Allah da suka yi suka samu babban rabo na shahada kuwa?
Ana Mazlum: Anya munsan girman matsayi da ladar wanda ya sadaukarda rayuwarsa a tafarkin Allah kuwa?
Anya muna daukar darasin abin da ya faru a baya da sauran masu gwagwarmayar tabbatar addini a duniya kuwa?
Anya ba za mu fito muce ma zaluncin nan zaluncin ya isa haka nan ba, mu tare a wuri mafi girma ga zaluncin azzalumai ba?
Anya idan muka farfado wannan lokacin ba za mu samu natija ba kuwa a daidai wannan lokacin?
Anya muna tsammanin cewa a daidai wannan lokacin wadannan azzaluman za su iya bude mana wuta a lokaci guda kuma subar sauran jama'ar gari suna irin nasu protest din kuwa?
Anya idan suka yi kuskuren bude wuta kuwa wani abu ba zai faru ba, ta yadda zai zama asasin tunbuke zalunci kuwa?
Anya idan muka kara jajircewa sauran jama'ar kasar nan ba za su antayo a cikinmu ba?
Anya kuwa mu da muke da Jagora daga Allah muke da addini zai yiwu ace a haka zamu yi tafiyar nan kuwa, anya ba za mu canza mu sake sabon lale ba kuwa?
Allah (T) yaji tausayinmu ya amfanar da mu.