Ana Jingina Dukkan Ya'yan Mace Ga Mahaifinsu Ne, Amma Banda Ya'yan Sayyidah Fatima (S.A) !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


NINE UBAN HASSAN DA HUSSEIN IN JI MANZON ALLAH (S. A. W. W) 


Imam Hassan da Hussein (A. S) 'ya'ya ne da suka fita dabam da dukkan wasu 'ya'yan baniy Aadama, domin zuriya takan sami daukaka ne ta bangaren nasabarta. 


Dukkannin 'ya'yan Annabawa (A. S) basu kai Imam Hassan da Hussein (A. S) ba, ko da kuwa 'ya'yan sun zama Annabawa Mursalai (A. S) ne. Kamar yadda Allah ya fifita Annabi (S. A. W. W) haka ya fifita 'ya'yansa akan kowa. 


Ku bi wannan riwaya dake tafe don ji daga Manzon Allah (S. A. W. W) 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



مُعْجَمُ الطَّبَرَانِيِّ بِإِسْنَادِهِ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ وَ أَرْبَعِينُ الْمُؤَذِّنِ وَ تَارِيخُ الْخَطِيبِ بِأَسَانِيدِهِمْ إِلَى جَابِرٍ قَالَ النَّبِيُّ ص‏

Ya zo cikin Mu'ujamud-'Dabaraniy da isnadi zuwa ga Ibn Abbas da ma masu riwayoyi Abba'in.


Sannan ya zo cikin Taarikhul-Kaden da isnadodinsu zuwa Jabir , yace, Annabi (S. A. W. W) yace; 


 إِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ جَعَلَ ذُرِّيَّةَ كُلِّ نَبِيٍّ مِنْ صُلْبِهِ خَاصَّةً وَ جَعَلَ ذُرِّيَّتِي مِنْ صُلْبِي وَ مِنْ صُلْبِ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ إِنَّ كُلَّ بَنِي بِنْتٍ يُنْسَبُونَ إِلَى أَبِيهِمْ إِلَّا أَوْلَادَ فَاطِمَةَ فَإِنِّي أَنَا أَبُوهُمْ.


" LALLE ALLAH (T) YA SANYA ZURIYAR KOWANNE ANNABI DAGA TSATSONSA NE KEBE (KHAAS), KUMA YA SANYA ZURIYATA DAGA TSATSONA DA TSATSON ALIYU 'DAN ABIY 'DALIB. 


LALLE DUKKAN 'YA'YAN 'YA (mace) ANA NASABTA SU NE ZUWA GA BABANSU, SAI DAI 'YA'YAN FATIMAH, DOMIN NI NINE UBANSU ."


__________________________


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 285


Tunda kuwa hakane dole ya zama wajibi ga dukkan mumini da mumina su nuna qaunarsu ga wadannan 'ya'ya don mai wannan magana , sannan su nuna baqin cikinsu ga duk abinda ya same su na cutarwa. 


Sai dai wani abin mamaki al'ummar da ke iqirari ne cewa wai wannan shine Annabinta amma tana farin ciki ko gaba da wadanda ke nuna baqin cikinsu da alhininsu game da abinda ya sami wadannan 'ya'ya wadanda babu kamarsu. 


Fatanmu shine Allah ya ganar dasu don a gudu tare a tsira tare. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

        (08126385470)


7th October, 2020/ 20th Safar, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post