@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HASKENSA YA RIQA JIJJUYAWA NE CIKIN TSARKAKAKKUN MAHAIFA
Halitta ta farko kuma mafi daraja cikin halittar Baniy Adama shine fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W).
Halittarsa ta faro ta kasance ne daga haske kafin halittarsa ta gangar jiki wanda ya fito qarqashin Adam (A. S).
Ya zo cikin Tafsirul-Furrata Bn Ibrahim Ja'afar Bn Muhammad Bn Bishrawaihi Al-Qaddanu, da isnadinsa daga Auzaa'iy, daga Sa'asa'ata Bn Suhaan, da Ahnaaf Bn Qaisin , daga Ibn Abbas (R. A) yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace,
" خَلَقَنِيَ اللَّهُ نُوراً تَحْتَ الْعَرْشِ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ آدَمَ ع بِاثْنَيْ عَشَرَ أَلْفَ سَنَةٍ فَلَمَّا أَنْ خَلَقَ اللَّهُ آدَمَ ع أَلْقَى النُّورَ فِي صُلْبِ آدَمَ ع فَأَقْبَلَ يَنْتَقِلُ ذَلِكَ النُّورُ مِنْ صُلْبٍ إِلَى صُلْبٍ حَتَّى افْتَرَقْنَا فِي صُلْبِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ وَ أَبِي طَالِبٍ فَخَلَقَنِي رَبِّي مِنْ ذَلِكَ النُّورِ لَكِنَّهُ لَا نَبِيَّ بَعْدِي[24]. ."
" ALLAH YA HALICCENI HASKE NE QARQASHIN AL-ARSHI SHEKARU DUBU SHA BIYU (12,000) KAFIN YA HALICCI ADAM (A. S) . YAYIN DA ALLAH YA HALICCI ADAM (A. S) SAI YA JEFA WANNAN HASKE CIKIN TSATSON ADAM (A. S) , SAI WANNAN HASKE YA JUYO YANA CIRUWA DAGA WANNAN TSATSO ZUWA WANNAN TSATSO, HAR MUKA RABU (ni da Ali) CIKIN ABDULLAHI BN ABDUL-MUDALLIB DA ABU 'DALIB.
UBANGIJINA YA HALICCE NI CIKIN WANNAN HASKEN NE, SAI DAI KAWAI BABU ANNABI NE BAYANA (da Ali ne zai kasance) ."
7) تفسير فرات: 207.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج15، ص: 7
MARABA DA ZUWA YAA TSARKAKEKKEN HASKEN DA YAFI KOMAI HASKE.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
08126385470
28th October, 2020/ 11th Rabi'ul-Awwal, 1442.