@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
RANAR DA ZAI DAMQE SHI NANAN KUSA
Yakan iya zama abin mamaki kuma batattu su qara bacewa cikin bata yayin da suka ga azzalumi na zaluntar raunana, su kuma raunana na addu'ar neman neman dauka musu fansa daga Ubangiji amma ba aga ijaba ta zahiri wanda kowa zai fahinta ba.
Babu irin nau'in zalunci wanda Buhari bai jarraba shi kan bayin Allah raunana ('yan Shi'ah ) ba, wasu na goya masa baya suna ganin abinda yake yi daidai ne, domin a imaninsu ya fi su tunani, ilimi, tausayi, sanin daidai, imani da kuma adalci , sannan kuma suna ganinsa a matsayin wanda ba ya kuskure.
Ta bangaren raunana wadanda ake zaluntarsu kuwa basu gajiya ba da yin addu'ah tare da haqurin zama cikin wannan jarrabawar da Allah yayi alqawarin jarraba su ita.
Kira kan nau'in mutane biyu nake son yi. Ku raunana raunana ku qara haquri da juriya har zuwa lokacin da Allah zai cika alqawarinSa na daukar muku fansa.
Ku kuma wawaye masu yaba masa kada kuyi tsammanin Allah ya yarda da abinda Buhari ke yi ne, domin Shi (T) ba ya zalunci kuma bai yarjewa bayinsa ba.
Ku biyo cikin wadannan ayoyi kuji abinda Allah ke fada a kansu.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ غَٰفِلًا عَمَّا يَعۡمَلُ ٱلظَّٰلِمُونَۚ إِنَّمَا يُؤَخِّرُهُمۡ لِيَوۡمٖ تَشۡخَصُ فِيهِ ٱلۡأَبۡصَٰرُ ٢٤
" KUMA KADA KAYI ZATON ALLAH MAI GAFALA NE GAME DA ABINDA AZZALUMAI KE AIKATAWA. ABIN SANI KAWAI YANA JINKIRTA MUSU NE ZUWA GA WANI YINI WANDA IDANUWA KE FITA TURU-TURU (don tsoro da firgici kamar wasu a ranar Ahzab) ."
مُهۡطِعِينَ مُقۡنِعِي رُءُوسِهِمۡ لَا يَرۡتَدُّ إِلَيۡهِمۡ طَرۡفُهُمۡۖ وَأَفۡـِٔدَتُهُمۡ هَوَآءٞ ٣٤
" MASU GAGGAWA (wajen neman wajen tsira), MASU 'DAUKAKA KAWUKANSU (zuwa sama), QIBTAWAR GANINSU BA YA KOMOWA GARE SU (don tsananin tashin hankali), KUMA ZUKATANSU WOFINTATTU !"
(Suratul-Ibrahim, aya ta 42-43)
To, wannan lokaci kawai ake jira kuma yayi kusan zuwa. Saboda haka ku sani ku da shi ba za ku tsira wajen Allah ba, domin duk mai goyon bayan azzalumi da zalunci shima azzalumi ne.
Daga nan ne Allah yake umartar ku da yi musu gargadi game da zuwan wannan rana don mai rabo ya kiyaye don ya rabauta.
وَأَنذِرِ ٱلنَّاسَ يَوۡمَ يَأۡتِيهِمُ ٱلۡعَذَابُ فَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ رَبَّنَآ أَخِّرۡنَآ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖ نُّجِبۡ دَعۡوَتَكَ وَنَتَّبِعِ ٱلرُّسُلَۗ أَوَلَمۡ تَكُونُوٓاْ أَقۡسَمۡتُم مِّن قَبۡلُ مَا لَكُم مِّن زَوَالٖ ٤٤
" KUMA KA YIWA MUTANE GARGADI GAME DA RANAR DA AZABA KE ZUWA MUSU (in sunyi zalunci), SAI WADANDA SU KAYI ZALUNCI (a duniya) SU CE, " Yaa Ubangijinmu ! Kayi mana jinkiri (dama wannan mutuwar da tazo mana yanzu) zuwa wani lokaci makusanci, mu karba maka kiranka (wanda ka kira mu a kansa kafin wannan lokaci), kuma mu bi manzanni (masu kargadinmu kan zaluncin da muke yi). (Sai Allah yace musu), " ASHE BA KU KASANCE KUNYI RANTSUWA BA KAFIN WANNAN LOKACI, CEWA BA KU DA QATA GUSHEWA (daga kan mulkin da kuke yi wanda kuke amfani da shi wajen zaluntar bayina) ?"
(Suratul-Ibrahim, aya ta 44)
Kirana ga azzalumai shine, tun ta wuri kafin lokaci ya qure muku ku fito ku nemi gafara daga wadanda kuke zalunta, kuma ku bar zalunci. Yin hakan zai sa Allah ya canza ayyukanku daga munana zuwa kyawawa. Kuma na san wadanda kuka zalunta din za su yafe muku, domin sun koyi yafiya daga Allah, Manzonsa da kuma A'immah (A. S).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(0812638547)
24th October, 2020/ 8th Rabi'ul-Awwal, 1442.