Akhlaq: Ta Hanyar Imfaqi Ake Ciyar Da Addini !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


A KULLUM MUNAFUKAI ZAGON QASA SUKE YIWA MUSLIMCI 


Kalmar IMFAQI tana nufin dukkan wani abu da za ka cire daga aljihunka ko dukiyarka ka bayar da ita wajen yin wani aiki wanda ya shafi addinin Allah ko kuma taimakawa wani don biyan buqatunsa. 


Wadannan ayyuka sun hada da :-


Gina makaranta, 


Gina masallaci,


Raya al'amarin Maulidi, 


Shirya (TABLIGH) isar da saqon Allah, 


Fadi-tashi (struggle) na neman 'yanci, 


Haqqin shahidai da sauransu. 


To, duk wadannan abinda muka lissafo a matsayin misali ba sa yiwuwa sai an sadaukar da wani abu daga cikin abinda Allah ya hore mana, kamar dai yadda babu dama wani abu na gida ya yiwu ba tare da an sanya kudi/dukiya ba. 


Annabi (S. A. W. W) yayi bayani a gurare da dama cewa addinnin muslimci ya kafu ne sakamakon ciyar da dukiyar Nana Khadijah (S. A) da kuma Takobin Imam Ali (A. S). 


Wadancan babban abin misali ne, amma Sahabban Annabi (S. A. W. W) sun taimaka sosai da dukiyoyinsu wajen cigaban addinin Allah. 


Sau da yawa idan wani aiki ya taso na zuwa Jihadi ne ko wani aiki na muslimci sai Annabi (S. A.W.W) ya tara sahabbansa ya kwadaitar dasu muhimmancin wannan aiki da kuma gudumowar da za su bayar don yiwuwarsa. To, anan ne kowa ke yin iya qoqarinsa ya bayar daga cikin abinda Allah ya hore musu. 


Wasu su bada kadan gwargwadon ikonsu, wasu su bayar mai yawa gwargwadon qarfinsu, wasu kuma nanan a gafe sun kasa bayar da kadan ballantana mai yawa, amma a hakan suna raina abinda wasu suka bayar, kuma suna zargin wasu da cewa don neman suna (riya) suke bayar da mai yawa. 


Yanzu haka ma akwai irinsu birjik cikin harka islamiyyah, sun noqe basa aiwatar da komai sai zargin 'yan'uwansu. 


Wadannan sune 'yan yiwa addini saddu, kuma Allah ya zarge su kan irin wannan aiki nasu. 


11 - باب في المجاهدة


حديث رقم :110


السادس عشر: عن أبي مسعود عقبة بن عمرو الأنصاري البدري رضي الله عنه قَالَ:



Ya zo cikin Riyadus-Saliheen cikin Babin Mujahada daga baban Mas'ud Uqbatu Bn Amruu Al-Ansariy Al-Badriyyu (R. A) yace, 



لَمَّا نَزَلَتْ آيةُ الصَّدَقَةِ كُنَّا نُحَامِلُ عَلَى ظُهُورِنَا، فَجَاءَ رَجُلٌ فَتَصَدَّقَ بِشَيءٍ كَثيرٍ، فقالوا: مُراءٍ، وَجَاءَ رَجُلٌ آخَرُ فَتَصَدَّقَ بِصَاعٍ، فقالُوا: إنَّ اللهَ لَغَنيٌّ عَنْ صَاعِ هَذَا! فَنَزَلَتْ: 

" Yayin da aka saukar da ayar sadaqa mun kasance muna daukar (kaya na imfaqi) a gadon bayanmu, wani mutum yazo yayi sadaqa da abu mai yawa, sai (munafukai) suce, " Kaga mai riya) , wani mutum na dabam yazo yayi sadaqa sa sa'i, sai (munafukai) since, " Allah wadatacce ne da wannan sa'in wannan (ba ya buqatarsa) ." Sai aka daukar da (aya), 


{الَّذِينَ يَلْمِزُونَ الْمُطَّوِّعِينَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ فِي الصَّدَقَاتِ وَالَّذِينَ لا يَجِدُونَ إِلاَّ جُهْدَهُمْ} 


" WADANDA SUKE AIBANTA MASU YIN ALHERI DAGA MUMINAI A CIKIN DUKIYOYIN SADAQA, DA WADANDA BASU SAMI (mai yawa ba ) FACE IYAKAR QOQARINSU , SAI SUNA YI MUSU IZGILI. ALLAH NA YIN IZGILI GARE SU, KUMA SUNA DA AZABA MAI RADADI. "

                  [التوبة : 79]. 


Anyi ittifaqi kansa, wannan lafazin Bukhari ne .


مُتَّفَقٌ عَلَيهِ، هذا لفظ البخاري.



Fadinsa cewa (Muna dauka) wanda aka yiwa Nunun dumma, da kuma Ha'un marar digo, ma'ana dayanmu yana a gadon bayansa don lada yayi sadaqa da shi. 


وَ(نُحَامِلُ) بضم النون وبالحاء المهملة: أي يحمل أحدنا عَلَى ظهره بالأجرة ويتصدق بِهَا.


Saboda haka irin wadannan mutane sune munafukai masu hana yin aikin alheri. A nisance su kuma kada ayi koyi dasu don babu alkhairi tare dasu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


           (08137925034)


31st October, 2020/ 14th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post