Sahabi Daga Bakin Sahabi Umar:- "A Bani Daya Daga Cikin Abubuwa Biyar da Aka Imam Aliy (as) Yafi a Bani Lahira !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


A BANI 'DAYA DAGA CIKINSU YA FI A BANI LAHIRA (IN JI SHI )


Allah (T) na ajiye baiwarsa ce a inda yaso, kuma akan wanda yaso ba tare da yin shawari ba. A duk lokacin da Allah yayi nufin baiwarsa ga mutum sai ya tattara masa abubuwa masu yawa na falala wadanda ko maqiyi ne sai yayi burin samun wani daga cikinsu. 


Cikin irin wannan baiwar tasa ce (T) ya kebanci Imam Ali (A. S) da wasu abubuwa biyar wadanda Umar Bn Khaddab yayi burin ina ma ace an ba shi ko da guda daya (1)ne daga cikinsu. 


كتاب الروضة يل، الفضائل لابن شاذان بِالْإِسْنَادِ يَرْفَعُهُ إِلَى عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ أَنَّهُ قَالَ:


Ya zo cikin Kitabur-Raudha, Fadha'il na Ibn Shazaan da isnadi wanda aka daukaka shi zuwa kan Umar Bn Khaddab yana cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 أُعْطِيَ عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ خَمْسَ خِصَالٍ لَوْ كَانَ لِي وَاحِدَةٌ[18] لَكَانَ أَحَبَّ إِلَيَّ مِنَ الدُّنْيَا وَ الْآخِرَةِ ."



" AN BAWA ALIYU BN ABIY 'DALIB WASU ABUBUWA BIYAR (5), DA 'DAYA DAGA CIKINSU YA KASANCE GARE NI DA NAFI SO FIYE DA (a bani) DUNIYA DA LAHIRA !"



 قَالُوا وَ مَا هِيَ يَا عُمَرُ قَالَ


Suka ce, menene su yaa Umar ? Yace, 



 الْأُولَى تَزْوِيجُهُ بِفَاطِمَةَ ع وَ فَتْحُ بَابِهِ إِلَى الْمَسْجِدِ حِينَ سُدَّتْ أَبْوَابُنَا وَ انْقِضَاضُ النَّجْمِ فِي حُجْرَتِهِ وَ يَوْمَ خَيْبَرَ قَوْلُ رَسُولِ اللَّهِ ص‏[19] لَأُعْطِيَنَّ الرَّايَةَ غَداً رَجُلًا يُحِبُّ اللَّهَ وَ رَسُولَهُ وَ يُحِبُّهُ اللَّهُ وَ رَسُولُهُ‏[20] يَفْتَحُ اللَّهُ عَلَى يَدِهِ‏[21] وَ اللَّهِ لَقَدْ كُنْتُ أَرْجُو أَنْ يَكُونَ لِي ذَلِكَ‏[22].



" NA FARKO SHINE; 


AURENSA DA FADIMATU (A. S), 


DA BUDE QOFARSA ZUWA MASALLACI YAYIN DA AKA TOTTOSHE (namu) QOFOFIN, 


DA FADOWAR TAURARO CIKIN 'DAKINSA, 


DA KUMA RANAR KHAIBAR (inda) ANNABI (S. A. W. W) KE CEWA,  


" GOBE ZAN BADA TUTA ⛳ GA WANI MUTUM 👨 WANDA YAKE SON ALLAH DA MANZONSA, ALLAH DA MANZONSA, KUMA SHI MA ALLAH DA MANZONSA NA SONSA, (Allah) ZAI YI BUDI A HANNUNSA ."


" Wallahi haqiqa nayi fatan hakan ya kasance gare ni (in ji Umar) ."

__________________________

(1) في المصدر: لو أراد.


(2) الفضائل: 159. و للعونى ايضا



Kaga kuwa duk wanda Allah ya tattarawa wadannan abubuwa biyar (5) har wani yayi burin ya samu daya (1) daga cikinsu ya fi a ba shi duniya da lahira ba zai taba zama kamarsa ba ballantana ma ace wai ya fi shi. 


Kuma har yana cewa ya sami abu (1) daga cikinsu ya fi a ba shi lahira. 


Wannan magana ta girgizani sosai, domin dukkan mumini burinsa shine ya sami lahira don ita ce dawwamammiya kuma mafi alkhairi ga komai. 


Amma sai ga shi yayi burin da an ba shi wani abu daga cikinsu ya fi lahirarsa. Shine nake tunanin ko Allah ya haskaka masa abinda zai samu a lahira basu kai wadannan abubuwa biyar din bane? 


Domin na san duk dadi ko ni'imar duniya bata kai ta lahira ba a gun mumini. 



Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

          (08137925034)


26th October, 2020/ 10th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post