Abin da ya sa muke yin tattakin Arba’in na Imam Husain

 



Taron Arba’in na Imam Husain (AS) a yanzu shi ne taron addini mafi girma a duniya, wanda yake zuwa kwanaki 40 bayan Ashura, ranar shahadar Imam Husain (AS), Jikan Manzo Annabi Muhammad (SAWA). A kowace shekara miliyoyin musulmi ne suke tururuwa zuwa birnin Karbala da ke Iraqi, inda nan ne kabarin Imam Husain (AS) yake don yin musharaka a tattakin wannan ziyara. 


Babbar manufar wannan tattaki shi ne tunawa da ji a jika irin wahalhalun da iyalan gidan Annabta suka fuskanta yayin da aka daure su da sarka, aka kada su cikin kukumi, huntu ba takalma a hamadar sahara mai zafi daga Karbala zuwa Damaskus da ke Siriya ta yanzu a kasa bayan kisan gillar da aka yi wa Imam Husain (AS) a shekara ta 61 bayan hijira. Wannan wani lokaci ne na jimami, bakin ciki da nazari kan wannan bakin zalunci da aka aiwatar ba kawai a falalin Karbala ba a duk fadin duniya.


Duk da haka muna sane da rashin fahimtar da wasu ke nuna mana saboda wannan tattakin da muke yi na Araba’in. Za mu so mu maimaita amsar da Jagoranmu da aka zalunta, wanda kuma yake tsare a halin yanzu, ya bayar a shekarar 2014 ga masu sukar mu. Ya ce: “Wadanda suke sukar tattakin nan kamata ya yi su zo su tambaye mu, me ya sa muke yin abin da muke yi, amma ba su zartar mana da hukunci kan abin da su ba su sani ba. In ba ka son abin da muke yi, to ka yi mana shiru, don kuwa da kafarmu muke yin tafiyar nan ba da taka ba. In ba ka son bakin kayan da muke sawa, to ka kyale mu, don kuwa a jikinmu muke sawa, ba a jikinka ba. Ba za mu taba tilasta maka ka yi tattaki tare da mu ba, ko ka sa bakin kayan da muke sawa, amma kafin mu yi haka nan, ka yi mana shiru kawai.”


Tattakin Arba’in na shekarar da ta gabata bai gamu da fushin mahukuntan kasar nan kamar yadda suka yi a shekarun baya ba tun bayan kisan kiyashin Zariya na 2015. Sai dai ba za mu manta ba cewa a ranar Ashura ta bana 1442 a duk duniya ba inda aka yi kisan kai in ban da a Kaduna, inda Gwamna Elrufa’ ke shugabanci. Don haka muna rokon Allah da ya kame hannuwan makiyanmu, kamar yadda ya kame hannuwansu a shekarar da ta gabata.


A fili yake cewa duk wani yunkuri na hana mu yin wannan tattaki na Arba’in na Imam Husain (AS) take mana hakkinmu ne na ‘yan’adamtaka, kamar yadda yake a cikin tsarin mulkin kasar nan. Ta yaya ma jama’ar da ba ta dauke da makami za a kira su ‘yan ta’adda ko ‘yan tashin hankali? Hakan bai taba faruwa a ko’ina ba in ba a Nijeriya ba.


Muna kara tabbatar wa jama’a cewa tattakin Arba’in na wannan shekarar, kamar sauran na baya ne, babu wani abin tsoro sai dai in jami’an tsaro ne suka haifar. Kuma tattakinmu na Arba’in ibada ne a wajenmu. A gane cewa son Imam Husain (AS) ba wani abu ne da ya kebanta da musulmi ba kawai tun a falalin da aka yi wa Imam Husain (AS) kisan gilla a falalin Karbala, amma na dukkan wanda yake son adalci, kuma yake fada da zalunci ne a dukkan zamani. 


A don haka muna kara jaddada kiranmu na a saki Jagoranmu da muke girmamawa, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda a yanzu ya shafe shekaru biyar cur a tsare ba bisa ka’ida ba, duk da cewa wata kotu ta ba da umurnin a sake shi. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai an saki Shaikh Zakzaky, matarsa da sauran ‘yan uwa musulmi da ake tsare da su tun Disambar 2015.


*SA HANNU:*

*SHAIKH ABDULHAMID BELLO*

08/10/2020 (20 ga Safar, 1442)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post