ISHAQ MUHAMMAD ISHAQ.
.
A irin wannan rana ce ta 14 ga Watan Safar na Shekara ta 38 bayan hijirah Muhammad bn Abibakar Dan Uwan Aisha Ummul Mu'uminina ya yi Shahada a garin Misra!, ta dalilin harin da Rundunar Mu'awiyya Dan Abu Sufyan suka kai masa a lokacin yana Gwamnan Misra ta bangaren Imamu Ali (as).
Muhammad dai 'Da ne a wajen Abubakar bn Abi Kuhafata, kuma Asma'u binti Umais ce Mahaifiyarsa. An haife Shi ne a Shekara ta 10 bayan hijirah a Garin Madinah.
.
Muhammad dai ya kasance daga cikin Manyan kebantattun Sahabbai kuma Mataimaka ga Amirul Mu'uminina Ali bn Abi Dalib (as), Kuma Imam (as) yana Son shi so mai tsanani, har ma a wani Zancen nasa yana cewa:
"Muhammad 'Dana ne daga tsatson Abubakar".
Littafin Sharhin Nahjul Balagah na Ibnu Abil Hadid al-Mu'utaziliy, Juzu'i na 6 Shafi na 253.
.
Haka ma a wani wajen Imam (as) yana fada dangane da Shi: "Hakika ya kasance Masoyi kuma 'Dan Reno a gare Ni"
.
Kuma lokacin da Labarin Kashe Shi ya riski Imam Ali (as) ya yi bakin ciki mai tsananin gaske!, yana cewa:
"A wajen Allah nake Neman Ladar sa, Shi 'Da ne mai nasiha, kuma Ma'aikaci mai kokari, sannan kuma Shi Takobi ne mai yankewa, kuma Gimshiqi ne madaukaki".
Littafin Al-anwarul Alawiyyah, na As-Sheikh Ja'afar an-Naqdiy, Shafi na 461.
.
SHAHADAR SA:-
A Shekara ta 38 ce Mu'awiyya ne ya tura Amru bn Ass zuwa Misra tare da Mayaka dubu hudu, tare da Mu'awiyyata bn Hudaij, da Abul A'awar as-Salamiy, suka rutsa da Shi, bayan da aka tarwatse aka bar Muhammad, ya fuskance Su da yaqi, sai Mu'awiyata bn Hudaij da Amru bn Ass suka kama Shi suka saka Shi a cikin Mushen Jaki suka qona Shi sai da ya zama gawayi! a Muhallin da ake kiran sa da 'KQUMU SHURAIK'. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun!!
Littafin Ansabul ash'raaf, Shafi na 403.
.
Kuma wasu masadir na Tarikhi sun nuna a lokacin da suka qona Shi din yana da ragowar Ransa bai karasa yin Shahada ba!.
Kuma Mu'awiyya ya yi farin ciki mai tsananin gaske da kashe Muhammad!. Shi kuma Amirul Mu'umina (as) ya yi bakin ciki mai tsananin gaske na rashin Masoyi kuma Mataimaki Wanda yake matsayin kamar 'Da a wajen sa. Kamar yanda ya fada a wani Zancen sa dangane da Shahadar Muhammad (R.A) yana cewa: "Mun girgiza a kan sa gwargwadon farin cikin Su, ban taba girgiza a kan Mutuwar Wani ba tun da aka fara wannan Yaqin irin girgiza ta a Kan sa ba!, ya kasance Dan Reno a waje na kuma ina lissafa shi a matsayin 'Da, ya kasance Mai biyayya kuma Dan Dan uwana". (Muhammad ya kasance Dan Uwan Abdullahi bn Ja'afar bn Abi Dalib ne ta bangaren Mahaifiya)
.
Kuma ta dalilin wannan Ta'adi na Mu'awiyya ne, Aisha Ummul Mu'umina Yar Uwar Muhammad ta tsani Mu'awiyya tsana mai tsananin gaske, domin ko magana ta ke idan ta cije sai yi addu'ar Tsinuwa kan Mu'awiyya!, kuma ba ta kara cin Gasasshen Nama ba tun daga Ranar har ta bar Duniya, domin ta kan tuna yanda Mu'awiyya ya sa aka Gasa Dan Uwansa yadda ake gasa nama a Wuta!.
Ko Shakka babu wannan aikin na Mu'awiyya ya munana ainun!, kuma aiki ne da ko a Jahiyya ba a San ana yin hakan ba!.
Muhammad (R.A) ya yi Shahada ne yana da Shekaru 28 a Duniya!.
.
Amincin Allah ya kara tabbata ga Muhammad Dan Abubakar, kuma tsinuwa madawwamiya ta kara tabbata a kan Makasan sa!.
.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com