Zuwa Ga 'Yan'uwa Muminai: Tabbas! Babu maganin da zai warkar da duniya daga rudani da zalunci da kuncin rayuwa sai musulunci


 

Allah ta'ala ya nuna mana haka, don haka ku zabura da sunan Allah don kubutar da kanku da kuma duniya baki daya. Babu abinda zai tseratar da duniya baki daya sai wannan sako na musulunci tare da gaskiya da adalci da kuma bada duk wani hakki mai shi.


Ya ku 'Yan'uwa! Kuji tsoron Allah, kada kuji tsoron kowa. Ku tsai da faralin da Allah ya wajabta maku na aiki. Ku nisanci sabon Allah da duk abin da shari'a ta haneku. Ku siffantu da siffofi kyawawa. Ku zama masu karfi da halayen ku na imani masu daukaka da abin da Allah yabaku na shiriya da izza da karanci.


Ku fuskanci Alkur'ani mai girma da gabobinku da zuciyarku. Kuyi riko da Alkur'ani da kuma iyalan gidan Manzon Allah (saww), domin shine abin da Manzon tsira Muhammad (s.a.w) yayi mana wasiyyah akai, kamar yadda ya zo a hadisin kakalaini.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post