Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad zarif ya bayyana cewa, babu bambanci a wurin Iran duk wanda ya ci zaben shugaban kasa a Amurka, matukar dai kasar tana kan siyasarta ta babakere da zaluntar al’ummomin duniya.
Zarif ya bayyana hakan ne a wata zantawa da kamfanin dillancin labaran sputnik na kasar Rasha a ziyarar da yake gudanarwa yanzua birnin Moscow, inda ya bayyana cewa siyasar Amurka ita ce tushen matsala.
Ya ce matsin lambar Amurka kan Iran ba sabon lamari ba ne, wannan matsin lamba ya fara tun fiye da shekaru 40 da suka gabata, wato tun daga lokacin da kasar ta zabi ta zama mai cikakken ‘yanci na siyasa ba ‘yar amshin shata ba.
Haka nan kuma Zarif ya yi ishara da cewa, abin day a rataya kan Amurka a halin yanzu matukar tana son sulhuntawa da Iran shi ne, ta zama mai bin dokoki na kasa da kasa, ta mutunta ka’idoji na diflomasiyya, ta daina yin shigar shugula a cikin harkokin cikin gida na kasar Iran, kuma ta koma cikin yarjejeniyar nukiliya kamar yadda aka rattaba hannu tare da ita.
A cikin shekara ta 2015 ne dai aka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, amma a cikin shekara ta 2018 shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga cikin yarjejeniyar, bisa zargin cewa Iran ta sabawa yin aiki da yarjejeniyar, zargin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA tare da sauran dukkanin kasashe da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar suka musunta, tare da bayyana cewa Amurka ta tafka babban kure.
Source: ABNA24.COM
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Labaran Duniya