@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KHUDUBAR IMAM ALI GA 'DANSA IMAM HASSAN (A. S)
Yana daga cikin khudubobin Imam Ali (A.S) wanda ya yiwa dansa Imam Hassan (A. S) wacce ta shafi kowa.
Karanta don ka amfana.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
قال علي لابنه الحسن رضي الله عنهما: يا بني، رأس الدين صحبة المتقين. وتمام الإخلاص اجتناب المحارم. وخير المقال ما صدقه الفعال. اقبلْ عذر من اعتذر إليك، واقبل العفو من الناس، وأطع أخاك وإن عصاك، وصله وإن جفاك.
FASSARA
-----------------
" YAA 'DANA! LALLE TUSHEN ADDINI SHINE YIN ABOTA DA MASU TSORON ALLAH, KUMA CIKAR IKHLASI (tsarkake aiki) SHINE NISANTAR ABUBUWAN DA AKA HARAMTA, KUMA MAFI ALKHAIRIN ABINDA MUTUM ZAI FADA SHINE ABINDA AIKINSA YA GASKATA SHI.
KA KARBI UZURIN WANDA YA KAWO UZURINSA GARE KA, KUMA KA RIQA KARBAR YAFIYA GA MUTANE , KUMA KA BAWA 'DAN'UWANKA KO DA KUWA YA SABA MAKA, SANNAN KA SADAR MASA (da zumunci) KO DA KUWA YA WOFINTAR DA KAI ."
(Mawa'izus-Sahabah)
Yin abota da masu tsoron Allah kan qarawa mutum tsoron Allah tare da nisantar aikata abinda aka haramta.
Mutum kan zama mutumin kirki ne in ya kasance aikinsa na zuwa daidai da abinda yake fada. Sannan yiwa mutum uzuri kan kawo maslaha a rayuwa, sannan yafiya abu ne mai kyau kuma wanda kowa ke son ayi mar.
Allah (T) na cewa;
" KUYI YAFIYA KUMA KU KAUDA DA, SHIN, KO BA KWA SO ALLAH YA GAFARTA MUKU NE ?"
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
22nd Sep, 2020/ 5th Safar, 1442.