Ga yanda zaman kotun yakasance ayau a kaduna:
Yau ma Allah ya sake dawo da mu Babbar kotun Jihar Kaduna in da gwamnati Jihar Kaduna ta kai Malam da mai dakin sa kotu kuma ta ke tuhumar su.
Idan ba manta ba, a yau kotun za ta ya yanke hukunci ne kan ko dai za ta saurari karar ko kuma ta yi watsi da ita karar.
Yanzu haka Malam da Malama Zeenat sun iso kotun.
Kamar kullum, AU Tumburkai ne zai kawo muku abubuwan da za su gudana kai tsaye.
Alkali ya shigo. Lauyoyi sun gabatar da kansu.
Alkali ya fara karatun hukunci
Alkalin ya bayyana cewa lauyoyin masu kariya sun nemi da a kori wannan kara bisa hujjoji 8 da suka gabatar cewa wannan Shari'a ta saba ka'idar tsarin mulkin Nijeriya. Sannan kuma shi kanshi laifin da aka ce an aikata tsarin mulkin Nijeriya bai san shi ba
*Alkali ya ci gaba da kawo bayanan da lauyoyin Malam suka gabatar don kare wannan bayanai Na su don yin watsi da wannan kara.*
*Ya ce wadanda suka gabatar da wannan quduri suna kalubatar wannan qara ne. Ya ce doka ta baiwa kowane wanda ake qada da ya qalubalanci tuhumar da ake masa. Ya ce lauyoyin sun bayyana cewa ba a karanta wa wadanda ake tuhuma laifin su ba. Amma ya ce a record din da ke gabansa an yi hakan.*
Ya ce lokacin da aka karanta tuhuma ga wadanda ake Kara ba su qalubalanci tuhumomin ba.
Don haka Alkali ya yi watsi da wannan da bukata a daidai wannan lokaci
[9/29, 9:52 AM] +234 803 469 1340: Amma ya ce ba za a yanke hukunci kan laifin da wadanda ake tuhuma ba su Riga sun ji tuhunar da ake musu ba
[9/29, 9:53 AM] +234 803 469 1340: Alkalin ya nemi da lauyoyin su zabi ranaku a jere masu yawa don kammala shariar cikin sauri.
[9/29, 9:54 AM] +234 803 469 1340: Yanzu lauyoyin su Malam sun ce karanta tuhumar yanzu. Sai a sanya ranar dawowa, su kuma lauyoyin gwamnati su kawo shaidun su
*An fara karanta tuhumar in da Mai karantawar ya ce "Kai Malam Ibraheem Zakzaky da Malama Zeenat da Malam Yakubu Yahaya Katsina da Sanusi..." sai Malam ya katse shi ya ce me ya sa ya ambato sauran mutane biyu. Sai Alkali ya ce ai ba su a cikin shariar.*
*Amma lauya Abubakar Marshall ya ce bai amince da cewa mutanen biyun ษoye bane. Don haka ya nemi da a cire sunan su.*
*Bayan karanta tuhumar farko. Malam ya Basu amsa da cewa rubbish and nonsense*
*Bayan karanta tuhumar farko. Malam ya Basu amsa da cewa rubbish and
nonsense*
Tuhuma ta biyu ma wadda a kan Sajen Yakubu Dan Kaduna ce. Malam ya sake Basu amsa da cewa rubbish and nonsense
*Tuhuma ta uku, ma the same answer. Ta hudu ma the same*
Tuhuma ta biyar, ta shida, ta bakwai da kuma ta takwas duk Malam ya ce same answer
Malam ya sa baki. In da ya ce alkalin ya yi excusing din su da zuwa kotu
Daga karshe dai Alkali Ya Dage Shariar zuwa Ranakun 18/19/ Nov.2020 Domin Yanke Hukunci
Bayan haka kuma bayan kammala zaman kotun a kaduna yan uwa sun fita zazzafar muzaharar freezakzaky a birnin kano ga kadan daga hotunan gurin muzaharar
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com