Yan uwa musulmi almajiran sayyid zakzaky(h)na garin malumfashi sunbayar da kyatar ledojin jini

Yanda yan uwa musulmi almajiran sayyid zakzaky(h) na garin malumfashi suka bayar da kyautar jini albarkacin imam hussain(a as )



Da safiyar yau Litinin 07/09/2020 ne 'yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na garin Malumfashi dake cikin Jihar Katsina suka yi ayari suka dunguma zuwa Asibitin Masu juna biyu da kuma Kananan yara dake cikin garin Malumfashi domin dibar jinin su da kuma bayar da shi kyauta ga al'umma marasa lafiya dake bukatar karin jini.

Jami'an kiwon lafiya na *"ISMA Medical Care Initiatives"* reshen karamar hukumar Malumfashi ne suka jagoranci dibar jinin da kuma damkashi ga hukumar Asbitin *"Maternal and Children Hospital Malumfashi"* domin bayar da shi kyauta ga majinyata dake bukatar karin jini.


Bayan 'yan uwan sun yi layi an debi jinin nasu, sai biyu daga cikin 'Yan ISMA na garin Malumfashi, Malam Ibrahim Jaji da Kamala Musa Nababa da kuma daliban Makarantar ISMA, Aliyu Nura Abdulkareem, Hajara Nura Abdulkareem da Siddika Yusuf suka damkashi ga hukumar Asibitin.

A yayin dibar jinin da kuma karbar shi, Alhaji Ya'u Hassan, wanda ya wakilci babban jami'in dake kula da bangaren dibar jini da gwaje-gwajensa a asibitin ya bayyana godiya da jin dadin su dangane da wannan aiki na sadaukarwa da 'Yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky na garin Malumfashi suka yi domin tallafawa al'umma marasa lafiya.

Da yake bayani a kan bayar da jinin, Malam Ibrahim Sanusi Jaji ya bayyana cewa sun bayar da wannan tallafin jini ne ga hukumar asibiti domin raba shi kyauta ga al'umma marasa lafiya a bisa Munasabar tunawa da juyayin Kisan Jikan Manzon Allah, Imam Husain (A.S), wanda aka yi wa kisan gilla aka kuma shekar da jinin sa da na 'ya'yansa da masoyan sa a filin Karbala.

Haka nan ya kuma bayyana cewa, bayar da jinin somin-tabi ne domin kuwa za su bayar da karin wani jinin ga karin wadansu asibitocin dake cikin garin Malumfashi domin taimakon jama'a marasa lafiya.

'Yan uwan da suka bayar da jininsu sun hada da: Mukhtar Musa Nababa, Zaharaddeen Lawal, Yahaya Bala, Muhammad Ibrahim Malinta, Usman Muhammad Imam, Abubakar Abdullahi, Mudassir Ya'u (Bara'a), Muhammad Nuraddeen Abdulkareem da kuma Husaini Kabir.


Wani abin sha'awa shi ne anan take tallafin jinin ya fara aiki a inda aka fara bayar da shi kyauta ga wata karamar yarinya wadda aka kawo asibitin mai Suna Azima Rabi'u daga Unguwar Baure dake cikin Karamar Hukumar Kafur wadda ke fama da ciwon Sikila.

Iyayen wannan yarinya sun bayyana godiyar su dangane da wannan taimako da aka yi masu. Haka zalika, jama'ar da suka shedi wannan lamari su ma ba a bar su a baya ba wajen yin addu'o'I na musamman ga wadannan 'yan uwa da suka bayar da jinin su domin tallafawa al'umma dama Jagoran Harka Islamiyya, Allamah Sayyid Zakzaky (H) wanda ya tarbiyyantar da 'yan uwa akan taimakawa da kuma hidimtawa al'umma.



*Daga Zaharaddeen Sani Malumfashi.*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post