ALLAH MUN KAAWO KAARAR #YAKUBU MUHAMMAD DA ABOKAN AIKIN SU,
Wasu bidiyoyi da hotuna na batanci da sharri da kaage da Kazafi akan Harka Islamiyya sun karade kusan Kowanne bangare na shafukan sadarwa na Yan uwa da mutanen Gari,
Bidiyoyin da'ake shiryawa a Karkashin wani kamfani dake Jihar Enugu a Karkashin Jagorancin Yakubu Muhammad
Ba komai ke cikin bidiyoyin ba Sai Baatawa Harka suna da shaafa Mata kashin kaaji
Abin Kunya daban mamaki shine yadda fuskar wannan bakin baawa Yakubu Muhammad ta fita a sahun masu Shirye~shiryen fina~finan
A cikin video din sun nuna wasu Mata marasa aikin yi da suka sallami iyayen su suka tafi yawon tambada da Mazaje masu Zaman kashe wando Dauke da Hotunan Sayyeed Allama Ibraheem Ya'aqoub Zakzaky (h)suna a sakar musu Mai Gidan su da wasu kalamai Sai wasu su Toni sojoji Sai su Kuma suyi harbi,
Kalli bidiyon
Bayan Haka sun fitar da Wata Mara rabo a duniya da lahira sanye da Buuje/Siket/Fatari Gwuiwoyin ta a waje Amma sanye da Hijabi a matsayin an harbi Sista Har jini Na Zuba daga jikin ta,Yana dakyau Yan uwa a Zurfafa tunani ayi abinda yadace,
Yana dakyau a maaka Shi Yakubu Muhammad din a Kotu,
Sannan Yana dakyau asan yadda Za'ayi a tsayar da Shirin fim din,ko a dakile yaduwar Shi dayawa a fadin Kasar inda daamar hakan,
Hakan Zai yiwune ta hanyar maaka Shi kanshi kamfanin a Kotu,
Yana dakyau yan uwa marubutan mu usamman bangaren masu rubutu da Yaren Turanci (English) suyi rubutun sanar da Al'umma Asalin Manufar wannan Shiri Na batanci,
Da Kuma kashedi da Jan kunne ga wannan bakin baawa Yakubu Muhammad
Daga Karshe muna Rokon Allah ya Tsinewa Yakubu Muhammad da ma'aikatan wannan kamfani da duk Wadanda suka fita a shirin da Wadanda suka biya Kudi a aikata batanci a kanmu
Abdullahi Ibraheem Isah Dabai
Tags:
Daga marubata