MA'ASUMAH HAUSA NIGERIAN NEWS UPDATES
Tare da Muh'd Aliyu Daud (Dansudan) Azare 070-32803940
Fa in fara da fadar Allah a Qur'ani inda yace *"Wamamin musibatin fabima kasabat aidikum...."* Fassara "Musiba Bata same ku ba sai sakamakon abinda da hannayenku suka aikata..."
Toh! shinan kowane cewa Sojojin wannan qasar bisa umarnin Buhari suka je Zariya suka kashe Mutane sama da dubu haka kawai don zalunci da qin addini! Sun yi kisa na rashin imani sosai, sun je da shirin yaqi, da manyan makamai kala-kala, daga ciki sunyi amfani da bom, da tankokin yaqi da Roket da Qurneti da sauransu, akan mutanen da basu da makami daga ciki akwai mata da yara da qananan yara! Sun qona Mutane da ransu! Sun wulaqanta Qur'anai! Hatta gawawwaki sun qona! Sun haqa rami guda sun binne su cikin dare ba Sallah ba wanka!, Sun binne Mutane da ransu! Sun harbi mata masu ciki zafin harbin yasa suka haifu a take suka kashe su suka kashe Jariran da suka Haifa suma basu barsu ba!
Wannan zalunci kowa yasan anyi shi ga Sheak Ibrahim Zakzaky(H) da Al-majiran sa a Zariya hatta shi kansa Basu barshi ba sun yi masa ruwan wuta gaba da gaba harbi shida Matarsa uwar dakinsa da nufin su kashe su, bayan sun kashe musu 'ya'ya uku maza matasa a gabansu bayan kuma ukun farko da suka kashe musu!
Sun yi hakane sabida yana qira ne shida Al-majiran sa zuwa ga adawo ga Littafin Allah a kuma yiwa kowa adalci, a bawa kowa hakkinsa, a dena zaluntar Mutane! Amirka da Ingila da Isra'ila su fice mana daga qasarmu! Su dena sace mana albarkatun qasa! Su dena assasa mana rigima da fada!, Inda ya tona asirinsu cewa sune Boko Haram ba kowa ba!!! Wannan yasa suka yi masa haka!
Har zuwa yau dinnan Gwamnatin Buhari take kashe masa Al-majirai a fadin qasarnan a ko'ina aduk sadda taso!
Kuma kowa ya yi qum, ya yi shiru da bakinsa! Dayawa ma suka ce abinda Gwamnati ta yi masa kuma take cigaba da yi masa shida Al-majiran sa ta yi dai-dai taci gaba da yi!
Sun riqeshi shida Matarsa cikin rashin lafiya na harbin da suka yi musu, babu magani! Duda umarnin kotu na a sake su, a biya su diyyar barnar da aka yi musu!
Amman Gwamnati ta yi biris da Umarnin ta take! Ta nuna ita ta fi qarfin doka da oda!
Kuma shima Al'ummah da yawa suka nuna ya yi dai-dai!!!
Toh don Allah ta ina Allah zai barku kuji dadi, ayi wannan zalunci kun goyi baya! Sai Allah ya barku kuji dadi ta Ina?
Dalilin wannan zalunci ne da goyon bayanku, yasa kuke cikin halin da kuke ciki! Na wahala da quncin rayuwa.
Kuma inde baza a saki Malamin nan ba! A kuma bi masa hakkinsa ba, wallahi musiba da bala'i da quncin rayuwa yanzu muka fara gani!.
Ku tuna da wannan qissosin:- Ta farko Karuwar da ta temaki kare ta bashi ruwa yasha a lokacin da yakejin qishin ruwa a sanadin haka Allah ya sakata a Aljannah!!!
Da kuma qissa ta biyu Musulmar Matar da ta daure kuliya, ta yi ta azabtar da ita, Wanda sanadin hakan yasa Allah ya sakata a wuta! Don azabtar da kuliya!
Ina kuma ga wanda ya kashe Mutum!?
Haka kuma wanda ya yi kalmar Shahada!!!
Kun manta fadar Allah ne inda yace "Duk wanda ya kashe Mumini yana sane sakamakon sa wutar Jahannama ce, kuma zai dauwama a cikinta"
Haka zalika Manzon Allah ya nuna Ka'aba yace "Ran Mumini daya ya fita"
Don Allah sai kuke zaton Allah zai barku bayan yaddar da kuka yi da murna da wannan zaluncin da masoyinku Buhari ya yi wa Sayyid Zakzaky (H) da Al-majiransa! Kuma yaci gaba da yi, yake kayin yi aduk lokacin da ya ga dama a ko'ina a qasarnan, kuma kuce Allah zai barku, ku sakata ku wala kuji dadi!, Haba wuce nan!
Allah in har baku dawo kunbi hakkin Sayyid Zakzaky(H) da Al-majiransa ba! Wannan shekarun gaba dinnan zaku gane da ruwa ake shayi! Kun rinqa ganin fitina da matsalar rayuwa kenan zaku dauwama a cikinta!!
Allah yana dan-dana muku wannan wahalar ne sabida ku gane kuskurenku!
Ku gane cewa kunyi kuskure na goyon bayan wannan zaluncin da aka yiwa Sayyid Zakzaky (H) da Al-majiransa sa! Kuma mafitar qasar tana HANNUNSA!
Qiransa ne Mafita gareku duniya da lahira!!!
Inda Allah yace Qur'ani *"Zaharal Fasadu fil barri wal bahari bima kasabat aydil nas liyuziqahum ba'adallazi amilu la'allahum yarji'un* Fassara "Barna da fasadi sun bayyana a doron qasa da cikin ruwa sabida abinda mutane suka aikata da kansu! Allah yana dan-dana musu hakane sabida abinda suka aikata wata qila ko zasu hankalta"
Allah yana muku hakane wataqila ko zaku hankalta ku gane cewa Dalilin zaluntar Sayyid Zakzaky (H) ne da Al-majiransa yasa kuka fada cikin wannan halin! Da kuma qin yadda da Qiran da yake yi ne, na adawo zuwa ga Littafin Allah! Shine mafitarmu duniya da lahira!!!
Shine kadai hanyar da zamu samu jin dadi anan duniya da lahira! Shine kuma hanyar da Allah yace mubi ba "Constitution" ba! Allah Yace mubi Littafin sa! Kuma qiran da Sayyid Zakzaky (H) ke yi kenan.
Kada mu manta wasu kadan daga cikin Malumai sun yi qira na a sake shi!
Inaga abinda suka hango Mana kenan! Na halin da qasar zata shiga Maluman irin su:- Sheak Dahiru Bauchi, Dr.Ahmad Gumi, Sheak Halliru Maraya Kaduna, da kuma Malam Idrees Dutsen Tanshi Da Sheak Abduljabbar da sauransu.
Mafitar qasarnan tana cikin sakinsa da bin hakkin zaluncin da aka yi masa da kuma qiran da yake yi ne!!!
Kuma shi dan gado ne, haka aka yiwa Annabawa ma!!! Ka binciki tarihi!!!
Ku ziyarcemu ta www.maasumah.ng.com don samun ingattattun labarai da Abubuwa masu amfanarwa!
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com