Tun Ranar Ghadeer Suka Yanke Tsammanin Nasarar Rusa Muslunci!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


WASU RIGAR MUSLIMCI SUKA SA DON CUTAR DA MUSLIMCI 


A ko da yaushe tarihi ne ke maimaita kansa, kuma ita sunnah ba a canza ta, mummuna ce ko kyakkyawa. 


Cikin kowacce tafiya ba a rasa wadanda suke wannan tafiya da mummuniyar manufa, kuma hakan ya samo asali ne daga wadanda su kayi tafiya tare da Manzon Allah (S. A. W. W). Wasu sunyi tafiya tare da shi ne don cimma wata manufa tasu ta duniya , sai dai Allah bai cika musu wannan buri nasu ba. 


Alqawarin Allah ne cewa zai cika haskensa ko da kafirai da munafukai sun qi. Wannan dalili yasa Allah ke danqa amanar jagorancin addininsa a hannun bayinsa salihai. 


Wannan hukunci na Allah ba ya yin dadi a wajen kafirai da munafukai, shi yasa a ko da yaushe burinsu shine suga bayan wakilan Allah na gari. 


Wasu a zamanin Annabi (S. A. W. W) sunyi burin wargaza muslimci in Annabi ya bar cikinsu, amma bisa iko nasa (T) sai ya miqa jagorancin addini a hannun waliyinsa Imam Ali (A. S) ranar Ghadeer. Tun daga lokacin munafukai suka yanke tsammanin nasara cikin muslimci, sai dai kawai gaba da qulla makirci ga bayin Allah. 


Shine Allah (T) ke cewa; 


" A YAU KAFIRAI SUN YANKE TSAMMANIN (nasara) DAGA ADDININKU (saboda haka) KADA KU JI TSORONSU KU JI TSORONA....."


        (Ma'idah, aya ta 3)


Kun san kafirai da munafukai makomarsu iri daya ce. 


To, yanzu wannan aiki ne kafirai da munafukai ke yin tarayya a kansa don wargaza muslimci ta hanyar qulla sharri/makirci ko kashe magadan Imam Ali (A. S). Saboda haka kada ku ji tsoronsu, ku tsoraci Allah kadai !


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


             09039791509


3rd Sep, 2020/ 15-2-1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post