Tausayin Talakawan Nigeria ne yake sa Buhari Kuka Kamar Yadda Talakawa Suka Rinka Yin Kuka Kafin Yahau Mulki..!!!


...Umar Hassan Gololo...

Dukkan abinda zai amfani talakawan Nigeria ya Zama bala'i da masifa a Wannan Gwamnatin da ta ci zabe da gagarumin rinjaye.

Dukkan Wanda yace rufe bodar Nigeria tana amfanar talakawan Nigeria kace karya yake Yi ko wanene shi.

Idan ka shiga kasuwa anan zaka gane Buhari Yana mulkin Nigeria, garin masara ya Zama turare Mai kamshin Dan goma, shinkafa mai tsakuwa ta Zama zinare,gero da dawa sun Zama sai wane da wane, garin rogo da dafaffen rogo sun Zama abin alfahari da ado a matsayin abinci.
Check-points na jami'an tsaron Nigeria sun Zama business center, jami'an tsaron Nigeria sun zamanto kamar dodanni a idon talakawa.

Hanyoyin mota sun Zama tarkon mutuwa, Asibitoci sun Zama Sansanonin Kare kukanka,akan Naira dubu ukun magani sai uwa ko 'ya'yanta su mutu.
Gidajen Jama'a da gonaki sun Zama dandalin Kidnappers.

A gida babu aminci a gona babu aminci,Kai hatta a makaranta Kidnappers suna Kai samame.
Menene abu kwaya daya Wanda yake amfanar talakawan Nigeria da Gwamnatin Buhari ta samar domin rama wa kura aniyarta na Miliyoyin kuri'un da suka jefa Masa.?
Haka za a cigaba da Zama karkashin jagorancin zalunci da azzalumai alhali ba su suka haliccemu ba.?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post