Ta Hanyar Yin Magana ake Sanin Mutum Shi Wanene !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


‏من أقوال الإمام علي عليه السلام:


Daga zantukan hikima na Imam Ali (A. S) yana cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" تكلموا تعرفوا ، فإن المرء مخبوء تحت لسانه ."


                 FASSARA 

               ------------------


" KAYI MAGANA ASAN (kai wanene), DOMIN SHI MUTUM ANA FASSARA NE TA QARQASHIN HARSHENSA. "


Wannan magana haka take, domin sau da yawa ba a iya sanin haqiqanin mutum shi wanene sai ta hanyar maganarsa. 


A fuska in kaga wani mutum za ka iya cewa shi mai hankali ne ko mai ilimi ko kuma mai wayo ne, amma ba za ka san haqiqaninsa ba sai ta hanyar furucinsa. 


Da zarar yayi magana ne za ka fahinci cewa ashe jahili ne tantiri. Wani kuma kasan cewa ashe cikakken mahaukaci ne. 


Akwai wani mahaukaci wanda a haka ba za ka iya fahintarsa ba har sai ta hanyar maganarsa. Wata rana ya roqi taimakon kudi a wajen dan'uwansa don ya shiga mota sai ya ba shi #200, shi kuma sai ya raina abinda aka ba shi. 


Da dan'uwan nasa yace masa ya godewa Allah fa ! Sai yace masa; 


" WALLAHI BA ZAN GODE MASA BA ! YAYI KOWA DA HANKALI NI KUMA YA YINI MAHAUKACI, TO, A HAKAN NE ZAN GODE MASA ? TO, WALLAHI BA ZAN GODE MASA BA !"


Saboda haka kowa akan gane shi wanene ta hanyar yin maganarsa ne. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


              08137925034


10th Sep, 2020/ 22nd Muharram, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post