Daga Zaharaddeen Mziag
Idan da zamuyi ɗan waiwaye da ake cewa adon tafiya kaitsaye zamuga cewa sharri akan mabiyin Annabi da Ahlulbayt na haƙiƙa wato (ƴan'shi'a) Asali yasamo tun bayan wafatin Annabi(S.A.W.W) Saboda Annabi (S) shi'aka fara yiwa.
MISALI:- Daga cikin sa shine: Bukhari ya riwaici Hadisi daga Anas bin Malik cewa, "Manzon Allah (S) ya kasance yana zuwa wajen Ummi Haramin Bint Milhan taciyar da shi abinci,(dayaci yaƙoshi sai ya kwanta) tasa hannunta tana gyangyaɗashi har yayi bacci zuwa can yafarka yana dariya (saboda wani mafarki da yayi). Sahihu Bukhari juz'i na 4, babi na 03 Hadisi mai lamba 2789 Shafi na 135.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una Annabin da yafi kowa kamala shi ake dangantawa da wan'nan mummunan aiki, bayan kuma har wayau acikin littafin dai na Sahihul Bukhari, ya riwaici wani ingataccen hadisi cewa Manzon Allah(S) yace kada ɗayanku ya keɓanta da wata mace ba tare da muharraminta ba.
Shin yanzu akwai wani malami mai mutumci da zai je gidan Almajirinsa ya iske baya nan, yasanya matar almajirin nasa tayimasa abinci ya zauna yaci har ya kwanta ya ɗora kansa akan cinyarta tana shafa kansa har yayi bacci?
Wan'nan sharri ne mafi muni da'aka ɗangata shugaban tsarkaka wanda yazo da saƙon shiriya Annabi Muhammad (S) dashi.
IMAM ALI ƊAN'ABI ƊALIBI MA BAI TSIRA BA.
Khalifan Annabi(S) na farko da ya nasabta'a matsayin magajin sa wato Imam Ali, ya fuskanci Sharri da ƙage domin sanya tsana a cikin zukatan mutanen zamanin sa, har takaiga idan ka faɗi wata Falala guda ɗaya ta Imam Ali hukuncin kisa ne akan ka, idan kuma hadisi ne na hukunci, sai ace bashi da inganci.
Ba don komi ba sai don shine mabiyin Annabi na haƙiƙa shine, sarkin yaƙin Annabi Bahrul Ilmi na manzon Allah.
Katambayi su Imam Nasa'i kasha labarin ƙiyayyar Ali a wajen mahukuntan zamanin sa, idan bakasani ba Shi Imam Nasa'i ankashe shi kisa na musla(andaddatsa shi) saboda ya rubuta Littafin falalar Imam Ali, yaƙi rubuta ta Mu'awuya.
Don haka wallahi billahil'azimi duk wanda yace zaibi Manzon Allah da Imam Ali bi na gaskiya sai sun kasheshi tun daga wancen zamanin har zuwa yau.
Kokuma su bishi da sharri da ƙage iri-iri domin jama'a su ƙyamace shi, ko kunmanta cewa mune akace munada Al'ƙur'ani namu na daban saɓanin na sauran musulmi? Ko kunmanta cewa mune akace muna zagin Sahabban manzon Allah(S)? Ko kunmanta cewa ance muna zagin matan Annabi? Ko kunmata cewa Ance muna Auren mutu'a (zina/bada aron matan mu)?
Wan'nan Shari gama gari kenan wanda ake jifar duk wani ɗan shi'a-aduniya dashi harda mu nan Nigeria, don haka kada kusha mamaki acikin wan'nan wasan kwaikwayon idan suka nuna irin wan'nan sharrin a cikin sa.
ABIN DARIYA:Har yau kasuwar taƙi riba, duk da maƙudan kuɗaɗen da suke kashewa wajen suga haƙarsu ta cimma ruwa.
Ina littafin Ayoyin Sheɗan na Farfesa Laɓɗo? Kunkau karantashi kunga abinda ke ciki? A'uzubillahi! Miyasa wasan kwaikwayo zaidameku, Eh tabbas abun takaici ne idan har abinda ake zargi na cin mutumci ya tabbata acikinsa.
Idan muka dubi irin shige da fice na ɓata suna da Gwamnatocin baya keyi akan bawon Allah muslihi Sheikh Dr Ibrahim Zakzaky, kuma idan mun tuna zamuga cewa wan'nan ba abin mamaki bane, kada inkaiku da nisa mukalli waƙi'ar zariya kawai alokacin da Gwamnati zata kawo hari, don Allah wan'nan ma ba film bane?
FILM NE SUKA SHIRYA KO NACE SHARRIN ZAHIRI. saboda ba'a fita film sai da kyamara da ƴan wasa kuma kowa da irin Role ɗin da zashi taka aciki, bakuga ƴan wasan su ba damakamai a gefe sunata kartar ƙasa waisu ala dole cikin mu suke? Bakuga Camera man ba da Darakta Kuka sheka? Ko bakuga furodusa Burtai ba a wajen? to wallahi bari kuji in faɗamaku da ba darana sukazo ba da har Lighters man(me bada haske) da fitilun sa sai yazo
Don film ɗin yafita da kyau. (Garau)
Amma da muka fitar da namu fa? Yauwa sai gashi cikin izza da nasara gaskiya ta kori ƙarya, bayan wan'nan kwanan nan fa sunje kaduna wajen da ƴan'uwa suke zaman juyayin Ashura, da nufin sake shirya wani film ɗin domin su ɓakanta harka da almajiran malam, Amma miyafaru? Sun ƙona motarsu ashe basu saniba ƙimar Gwamnati ce suke ƙara ƙonawa.
Bayan sungama ƙonawa miyafaru?
Kuce mani kinya suka ɗiba
Kada fa kumanta a Abuja har kumandan su na ƴansanda suka kashe a zahiri domin suƙara ɓata Harka amma duniya ta gane ƙarya suke, to balle a Fim wanda koda za'a kalla amatsayin ana kallon wasan kwaikwayo ne.
Banmantawa alokacin muna yara idan mukaga ankashe awani a film ko anji masa ciwo sai muji tausayin sa ya kama mu, idan ma har akwai abin ban tsoro aciki sai mukasa fita waje sai manyan mu suce, kai dawasa fa ake duk shirine.
WALLAHI DA SUNYI NASARAR ƁATA HARKA BAZASU TAƁA ƘIRƘIRAR WAN'NAN FILM ƊIN WASAN KWAIKWAYON BA, Abun da kawai zasuyi shine, su ida kwangilar da suka karɓo.
Wan'nan ma ni, saiya ƙara nuna mani cewa lallai Sheikh Dr Ibrahim Zakzaky (H) Ikon Allah ne waliyin Allah ne, idan ma zasuyi domin su jama harka baƙin jini to sai muce bisimillah.
Munga wani Film da NTA ta taɓa shiyawa aka gaiyato wasu uztazai masu rawanin (Izala'shi'a)
Suka fara Comedy aƙarshe suka fita babu nauyi.
Shi kansa wan'nan film ɗin da ke cike da zargin Nasiru me gurfani ne furodusa, bara kuga yanda za'aƙare, bakuga ya tara manyan mashawarta ba acikin fadarsa harda tsohon sarki, da masu ɗangalallen wando ƴan inada nera? Kwaji sauran zancen.
To dai, da incikaku da surutu kujira kuga wasan inda zaikai su, suyi amfani da kuɗin su suƙarama malam da almajiran malam farinjini.
Inji wani mawaƙin harka yace: (Da kuɗin ku kunjawo mar farinjinin duniya)
Insha Allah zanyi rubut na 2 idan dama ta bada amma dai wan'nan Torchlight ce mai batir biyu na haska idon maƙiya Allah.
Dafatan Allah ka ƙara tsare mana maulam mu jagoran mu murshidin mu zuwaga manzon tsira (S) Sheikh Dr Ibrahim Alzakzaky(H)
#Freezakzaky!
#Freezakzaky!!
#Freezakzaky!!!
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com