RASUWAR SARKIN ZAZZAU: Almajiran Shaikh Zakzaky Sun Kai Ziyarar Ta’aziyyah



Daga Ammar M. Rajab


Da ranar yau Talata 22 ga watan Satumban 2020, ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka kai ziyarar ta’aziyyah zuwa ga Masarautar Zazzau bisa rasuwar mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr) Shehu Idris.


Ziyarar ta gudana ne a karkashin jagorancin Shaikh Abdulhamid Bello, inda masarautar ta karbe hannu bibbiyu tare da ba su wurin zama kafin a gabatar da su ga sauran wadanda suke wurin ta’aziyyar.


Ciroman Shantali (Protocol Officer) na Masarautar Zazzau shi ne ya gabatar da tawagar almajiran Shaikh Zakzaky ga Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, da kuma Sarkin Jema’a da sauran tawagar masu karbar ziyara a madadin masarauta da iyalai.


Daga cikin tawagar almajiran Shaikh Zakzaky sun hada da Fasto Yohanna Buru, Abujihad, Alhaji Mansur Samaru, Malam Maiwada, Alhaji Tukur Alhazawa, Malam Musa Gambo, Malam Muhammad Inuwa, sai kuma tawagar Media Forum na Zariya, wakilan Harisawa da dai sauran su.


Shaikh Abdulhamid Bello ne ya gabatar da makasudin zuwa wannan ziyara, inda ya bayyana musu cewa; “mun zo ne domin mika sakon ta’aziyyarmu bisa rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau.”


Tun a farkon jawabinsa ya lurantar inda ya kawo ayar Alkur’ani da yake nuni da cewa; dukkanin wata rai sai ta dandani dacin mutuwa. Sannan ya mika sakon ta’aziyyarsu a madadin Shaikh Zakzaky bisa rasuwar Sarkin na Zazzau.


A karshe aka yi addu’a ga Marigayin, sannan tawagar ta fita daga fadar Masarautar Zazzau da misalin karfe 3 da mintoci na yammacin yau


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post