YANDA TURAWA SUKA RUSA DAULAR SHEHU USMAN DANFODIO SUKA KAFA TASU
Daga Sheikh Ibrahim Zakzaky (H)
Matuqar qasar nan ta wanzu lallai bata wanzu domin amfaninmu ba, kuma baza ta taba amfanarmu ba har abada, har sai mun kafa namu. To tambaya, kafin Bature yazo kakanninmu basu kafa qasa bane? Sun kafa!! Ko kun manta da jahadin Shehu Usman Danfodiyo ne?, shekara dari (100) kafin zuwan Bature, an kafa daula a asasin imani, shi kuma Bature da ya zo ba babarodo yayi mana ba, balo-balo yayi wannan abun, ya tabbatar da cewa ala dole sai ya ci Sokoto da yaki, yayi marching yaje Sokoto, ya rutsa da Sokoto ya shiga ta kofa guda, ashe ya yiwa mutane abin da ake cewa "kofar rago" duk kofofin fita garin ya je an sa sojoji sun yi kwanton bauna, da wuta yayi wuta ta kofar da suka shiga ta kofar Taromniya, duk wanda yayi gudu sai a harbe shi. Don sojoji sunyi kwanton bauna ta duk sauran kofofin garin, duk wanda ya fita sun harbe, ba wanda ya saura. Wanda shi sarkin Musulmi Attahiru bai iya fita ba, ya fita kafin suje garin ne, kuma suka bishi suna neman sai sun yaqe shi, har suka cimmasa a Barauni, kuma su kayi kisan Gilla sai da suka loda gawawwki, sai da suka yi dala ko nace daloli na gawawwaki.
Sannan bayan sun tabbatar da cewa sun rusa wannan, sun yi kisa, sannan Lugard ba tare da ya boye ba yayi jawabi a Sokoto, ranar 15 ga watan Maris, dubu da dari tara da uku, yace "Da chan Fulani sun ci kasar nan da yaki saboda haka su suke da ikon su mallaketa, amma mu yanzu turawan Ingilishi mu kuma mun ciku da yaki saboda haka mu keda hakkin mallakarku. Mun san kuna da dokoki irin naku na addininku, muma muna da dokoki irin na addininmu. Akwai bukatan ku fahimci irin namu addinin da dokokin don shine yanzu zai mallake ku". Kuma har ma yayi dokokin Ingila da larabci, akwai wani littafi da naga an rubuta da irin rubutunmu, da arabiya, ana gaya musu yanda tsarin mulkin Sarkin Ingila yake, don su fahimci yanzu sun koma karkashin Ingilishi.
Kuma har wala yau bayan Lugard yayi wannan aka yi wani biki a ranar 4 ga watan Aprilu na dubu da dari tara, aka yi Biki a Lokoja duk ya tara Sarakunan da ya cire su daga Sarauta da malaman da ya kamo, yazo dasu aka tara su a Lokoja a wani wuri aka yi musu bayani, aka ce musu " Da chan kunga tutar ku, aka dauko tutar Danfodiyo , tutar Danfodiyo yana da La'ilaha'illallah Muhammadu Rasulillah a cikinta, akace da karkashin wannan tutar kuke, amma yanzu bari kuga makomar tutar, aka kawo wuta aka cinna. Sannan aka dauko tuta mai Cross na Ingila aka daga aka ce yanzu kuna karkashin wannan tutar ne, duk sarakunan suna ji.
Aka ce kuma a dauko Al'qur'ani aka ce da chan wannan shine dokarku, amma yanzu bari kuga makomarsa, aka dauko wani tsinannen Bature ya kware azzakarinsa ya tsulalawa Qur'ani fitsari. Wannan ya auku ne, karanta tarihi ka gani, suka ce to daga yau dokar Qur'ani ya kawo karshe. To kunga ya boye? Ina tambaya ya boye? Sai ya nuna muku yanzu kuna karkashinsa ne.
Wannan al'amari ya chanchanci ace kuka muke yi, amma sai muka wayi gari mutane na alfahari da Bature wai ya kawo adalci ne, wai ya kawo Ilimi. Har ma aka yi wani sarkin Musulmi ya zabi ranar da aka ci Sokoto da yaki a ranar da za ayi bakin nada shi Sarki. Ya kuma fada a cikin jawabinsa cewa "Na zabi ranar 15 ga wata domin ya dace da ranar da Bature yaci Sokoto" kaga abin alfahari ne cin Sokoto da yaki. Kuma aka yi fira dashi a BBC yake cewa "Ai zaben Sarkin Musulmi ma sai Sarauniya ta yarda, kai kace abin kirki ne har alfahari suke sun zamo karkashin Sarauniya.
Kuma kar ka ce min ba addini bane sai dai in kai qidahumi ne, ko kobonka mai bankaura, mai huji, in kana nan dashi dauko shi ka duba, kan sarki da dammara, duba kan sarkin zaka ga Cross, duba dammarar, dammarar yahudu ne. Kar kace min ba addini bane, addininsa ya kawo.
- Wani bangare na Jawabin Sheikh Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky (H) a shekarun baya.
- Ibrahim Almustapha Saminaka ya Naqalto muku