Mutum 'Daya Ya Shiryu Ta Hannunka Yafi A Baka Garken Raquma!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

HAR YANZU MUNA HALIN DA'AWA NE BA 'DAUKAR MAKAMI BA 

yanzu babban aikin da ya hau kanmu shine isar da saqon Allah ta hanyar koyarwar Manzon Allah (S. A. W. W) da iyalan gidansa (A. S). 

Anzo gurin, wato lokacin da miyagun malamai suka yawaita, malaman kirki su kayi qaranci, sannan jahilci ke tashensa. Ka san ba yawan karatu ne ilimi ba, a'a, aiki da shi shine ilimin.

Akwai bayin Allah masu neman shiriya amma sai suka fada hannun masharranta masu sharara qarya da sunan addinin gaskiya. 

Saboda haka ya zama wajibi mu tashi don yin kira birni da qauye, tudu da gangare don ceto wadannan bayin Allah masu neman tsira, amma kiran ya kasance cikin hikima. 

Har yanzu bamu iso lokacin daukar makami ba, shi yasa bamu taba jin Sayyid (H) yayi da'awar hakan ba. Mu saurari abinda Annabi (S. A. W. W) ya fadawa Imam Ali (A. S) cikin wannan hadisi. 

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

Manzon Allah (S. A. W. W) take, 

" GOBE ZAN BADA TUTA GA WANI MUTUM WANDA ALLAH ZAI YI BUDI A HANNUNSA ."

sai mutane suka wayi gari suna kai-kawo cikin dare ko waye za a bawa daga cikinsu. 

To, a yayin da gari ya waye sai mutane su kayi sammako zuwa ga Annabi (S. A. W. W), kowanne na burin a ba shi, sai yace; 

" INA ALIYU BN ABIY 'DALIB ? " Suka ce yana fama da ciwon ido yaa Ma'aikin Allah. Yace; 

" KU JE KU ZO MIN DA SHI. "

To, a lokacin da yazo sai (Manzon Allah) yayi mar tofi a idanunsa yayi mar addu'ah, sai ya warke tamkar wata jinya bata same shi ba, sannan ya ba shi Tuta. Sai Imam Ali (A. S) yace; " 

" YAA MA'AIKIN ALLAH, NA YAQE SU HAR SAI SAI KASANCE MISALINMU ?" Sai yace; 

" JEKA AKAN SHA'ANINKA HAR SAI KA SAUKA A FARFAJIYARSU , SANNAN KA KIRA SU ZUWA MUSLIMCI, KUMA KA BASU LABARIN ABINDA YA WAJABA A KANSU DAGA HAQQOQIN ALLAH. NA RANTSE DA ALLAH, DA ACE MUTUM 'DAYA ZAI SHIRYU TA HANNUNKA YAFI ALKHAIRI GARE KA DAGA GARKEN JAJAYEN RAQUMA SU KASANCE GARE KA ."

      (Bukhari, hadisi na 3701)


Tare da Ado Isah Guda. 


            09039791509


4th sep, 2020/ 4-2-1442

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post