Musibar Ambaliyar Ruwa A Jahar Sokoto !!!


Daga Halidu Shaheed Usman A

Al'ummar jahar Sokoto bangaren Sabon Birni, Goronyo da Wurno Takakume dss, suna fama da matsalar Ambaliya Ruwa a duk garuruwan da suke kusa da Gulbi (kogi). Wannan Ambaliya Ruwa ta lalata mafi yawan albarkun Gona (Abin da aka shibka) duk sun lalace, kuma ruwan kari kullum sukeyi ba ragi ba. Yanzu halin da ake ciki ba ma kayan Gona ake magana ba, yanzu ruwan suna kokarin su tayar da wasu garuruwa ne daga inda suke zaune. W
asu garuruwa suna nan suna kwasar kayansu suna barin gari, wasu kuma suna komawa wasu shiyoyi domin su tsira da rayukansu. Garuruwa da dama basu taba samun ambaliyar ruwa ba sai wannan shekara, wadan da ma sun saba ganin ambaliya cewa suke "radda Allah ya yi su basu taba ganin irin wadannan ruwa ba". Da yawan Garuruwan da wannan Ambaliya ke damun su basa kwana, kullum dare da rana kashin ruwa kawai sukeyi domin su samu su tsira da muhalan su, wasu ma tuni ruwa sun rosa gidajen su saboda sunyi iya kokarin su na hana ruwa shiga cikin gari amma ruwan sunfi qarfin su. Wadannan Al-umma suna neman agaji na gaggawa daga Gwamnatin Tarayya da ta Jaha da yan siyasa da ma masu kudi domin yin ganuwa wadda zata hana ruwa shiga cikin garuruwa su.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post