Mu Ba Zanga-Zanga Mike Ba , Muna Muzahara Ne !!!



"To, in sun gan mu muna taro, sai su dauka mu ‘crowd’ ne. To, shi ‘crowd’ shi ne ainihin, shi yana daga cikin dabi’arsa, mun karanta a ‘sociology’, ‘characteristic’ din ‘crowd’, akwai daga cikin cewa; shi ‘crowd is a leaderless’, ba shi da jagora, saboda haka, daga cikin dabi’arsa shi ‘emotional’ ne, galiban sa, saboda haka idan mutum zai jagoranci ‘crowd’ yanka ihu zai yi. Zai ce; a yi kaza neeee, sai kawai shi ke nan, sai kawai; yeeee, kawai sai a shiga yi.

"Saboda haka idan mutane suna zanga-zanga, wanda a kan titi suka hadu, wanda ake ce ma zanga-zanga, dan haka ma muka ce; mu ba muna zanga-zanga ba ne, muna muzahara ne! Muna bayyana wani abu ne, ba muna zanga-zanga ba ne! Zanga-zanga kawai an rude ne kawai aka bayyana a bakin titi. To, yanzun nan duk wanda ya iya yanka ihu shi ne jagora. Sai ya kamfaci wani. In ana nan ana cikin wannan, sai wani Dan sanda ya ce; a buge shi ne, sai ka ji ka-ka-kaf, kai ku daina ya isa haka nan. Wani ya ce; kai kashe shi ya kamata a yi, sai ka ji ka-ka-kau, to, shi ke nan, ‘crowd’ ke nan. Shi kawai bai da kan-gado. Shi kawai ba shi da jagora kuma ‘emotional’ ne kana iya juya shi yadda ka so.

"To, su jami’an tsaro har yanzu suna kallon mu ‘crowd’ ne, sai su zo su yanka ihu, ta nan ne ma muke gane jami’in tsaro. In ka ji mutum ya yanka ihu Malam ya ce; heee, a yi kaza neee! To, dube shi da kyau, za ka gan shi ko da gemun roba ko kuma bayi da shi ya share, ya yi wani kamannu, wato ainihin dama daga Bariki ya zo. Wai shi ya dauka ‘crowd’ ne zai ja ‘crowd’ din ya riske shi ya yi yadda ya ga dama. "


*— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a ranar Asabar din 26 ga watan Zulkada, 1435 (20/9/2014) a muhallin Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. A lokacin mu’utamar din Tattaki da Ashura na yini daya karo na farko.*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post