Mene Aibin Yada Hotuna Ko Bidiyo Na Sharrin Da Akai Mana – Cewar Abbagano



Nakanga ƴan uwa da daman gaske suna tacewa mudaina taya jahiliyya yaɗa hotuna da sharrin dasukai!!!


To kai mai faɗar hakan idan abin mu tambaye kane, tayaya kasan abin ya faru? 


Idan mukai shiru bamu yaɗa mutane dayawa sun gani ba to tayaya masu zurfin nazarin dake cikin mu zasuyi nazari kan hakan?


Bawai kawai muna yaɗawa bane, muna bayani ne domin mutane su fahimci irin shirin da ake mana, ta yadda idan abin yazo su san mundaɗe da barranta da Abin!!!


Su Sayyid suna bamu labarin shirin da azzalumai suke yi, akan harka islamiyya, to wannan ma taya su yaɗawa ne?


Hakan yana nufin ƴan uwa su shirya domin su san ana mugun shiri akan su, Sannan mutanen gari ma su san akwai abinda ake shirya wa akan mu!!!


Ta hanyar yaɗawa ne ƴan uwa dayawa zasu gani suyi Allah wadai da abin!!!


Ta hanyar yaɗawa ne su azzaluman zasu san ansan mesuke kuma ga irin matakan da ake ɗauka!!!


Ta hanyar yaɗawa masu nazari zasu nazarci Abin Domin gane hadafin azzalumai!!!


Ta hanyar yaɗawa ne masu matsayin dake cikin mu zasu farka don yin abinda yake gaban su!!!


Ta hanyar yaɗawa ne masu baccin cikin mu zasu farka don su san akwai shirin da akeyi a kansu!!!


Wannan fahimta tace bawan Inna nufin lalle itace daidai ba!!!


Abbagano ✍️

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post