~Malam Adamu Jaji Maji
Daga: Abubakar Muhammad Barde Alpotiskumy
An haife ta ne a gidan Annabta, Fatima ta taso ne a gidan Annabta sannan kuma a gidan da ta rayu a nan wahayi yake sauka kuma Baban ta yace Daga Allah: Fatima itace shugabar ko wace mace a Duniya duk iliminta duk matsayin ta duk kyawunta,
Sannan kuma ance Baban ta shine birnin Ilimi, mijin ta kuma kofar Ilimi to me yasa duk da irin wadannan abubuwa sai ya zamanto aka ce ita bata da ilimi
A yanda muka gani a tarihin magabata wadanda su kayi aiki a addini babu wata ruwaya da aka kawo na maganganu akan Ilimin ita Fatima kuma babu wani abu da muka gani akan tarbiyyar da fatima ta koyar akan 'Ya 'yan ta wanda yanzu idan ana bukatar a koyi tarbiyya za'a duba littattafai ace ga abinda Fatima ta koyar da ya'yan ta saboda ita Manzon Allah ne yayi mata tarbiyya za'a koyi tarbiyya daga gare ta amma babu.
Sannan tayi aure kuma babu wasu hadisai da aka kawo wanda suka koyar aka ce wadannan hadisai daga Fatima ne wanda ya kunshi tarihi na irin zaman auren da tayi da Amirul Muminin, irin yanda baban ta yayi mata tarbiyya irin na zaman aure gashi an tambaye ta duk ta bada labari amma babu.
Anya kuwa babu ayar tambaya a ciki?
Mun san akwai matar da sai da ta isa aure sannan Annabi ya aure ta amma saboda tsantsar Ilimi da yake sauka a gidan Annabi da kuma shi Annabin kan sa, sai ya zama duk wani abu na tarbiyya da duk wani abu na tarihi akwai ruwayar sa a wajen ta kuma an karba kuma muma mun karba saboda ta zauna da Manzon Allah (S) kuma wahayi a gidan yake sauka kuma Manzon Allah shine birnin Ilimi sannan shine ma taskar ilimin Allah ma gaba daya
Kaga idan aka ce matar sa ta zamanto mai Ilimin ko wani abu na Duniya tana da abun cewa a ciki ba abun mamaki bane,
To amma abun mamaki shine ita Fatima fa? Me yasa ita Fatima babu wannan? Alhali tun lokacin da aka haife ta har ta kai shekarun aure tana zaune a gaban baban ta kuma kafin a haife ta ma wahayi yana sauka duk sauran wahayi ya sauka a gaban ta tana zaune a gaban baban ta wahayi yake sauka amma gaba daya bata ruwaito komai ba,
Kun ga wannan abun akwai abun mamaki a ciki, sannan kuma da ta tashi daga gidan Manzon Allah (S) baban ta ba wani waje aka kai ta ba face wajen da aka ce wanda zai rike ta shine kofar ilimin Manzon Allah (S) to wai ma a hakan ma bata san komai ba alhali ga can wasu wanda suka zauna da masu Ilimi sun zo sun bada ruwayoyi daban daban duk abinda ake nema na Ilimi wajen su ake zuwa amma ita Fatima fa? Babu wannan
Wannan abun akwai tambaya a ciki sannan kuma meye dalili?
Wani Bangare Na Jawabin Malam Adamu Jaji Maji A Wajen Maulidin Sayyida Zahara Wanda Yan Unguwar Radawiyya Suka Gudanar A Potiskum A Shekarar 2018.
Tags:
Filin Sayyadah Ma'asumah