INJI BABBAN MASOYIN BABA BUHARI MUSA IBRAHIM DAURA (SARKIN NOMA)
Dazu ne na saurari wata hira A BBC HAUSA SHIRIN HANTSI, da akayi da MAWAKIN NAN Dauda kahutu Wanda akafi sani da suna RARARA.
A cikin hirar ne yake cewa ya dainawa shugaba Buhari waka, sakamakon cewa da akeyi Buhari ya rasa masoya da dama, Don haka yanaso ya nunawa duniya har yanzu buhari yana da masoya, Saboda haka sai talakkawa Sun tura masa naira dubu dubu a asusun banki sa kafin yawa buhari waka. Wai don asan masoyan Buhari suna nan, Tab! Kada Allah yasa kayi wakar.
Inaso in sanar da Rarara ko ya yarda ko kada Allah yasa ya yarda TABBAS BUHARI YA RASA MAGOYA BAYA SOSAI sakamakon rashin tafiyar gwamnati yadda akayi zato, wahalhalu Sun dabaibaye mutane ta kowace fuska. Gwamnatin buhari ta gaza gazawa ta Hakika. Wannan yasa akarasa magoya baya.
Don haka ina kira ga ma'abota hankali suyi watsi da Wannan bukata ta Rarara kada Allah yasa yayi wakar, idan yayi wakar wata tsiya zata amfanawa kasa da Mutanen kasa? Da Can dayake samun kudin banza miyasa bai fadi haka ba.
Ina kuma so mutane su gane Cewa wannna bakauyen raina hankalin ku zaiyi, wata kila wata hanya ce yakeso yabi ta hanyar tarawa kansa kudi. Misali mutum miliyan daya idan suka bashi naira dubu daya daya, wato zai samu naira miliyan dubu kenan (biliyan daya). To abin tambaya kudin daya samu a baya mi ya amfanawa talakkawa?
Daga karshe Don Allah Rarara kada ka karawa shugaba buhari waka daga yau, idan kakiyi sai wata tsiya? Aikin banza aikin wofi BATURE YAGA ZAGI.
MUSA IBRAHIM DAURA
11/9/2020
Tags:
Daga marubata