@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
من أقوال الإمام علي عليه السلام:
Daga cikin zantukansa na hikima (A. S) ya bayyana matsayin duniya a wajen Allah yadda yake siffanta ta a matsayin qasqantacciya wacce ake cikata da sabon Allah, kuma ba a samun sakamakon Allah kan ayyukan da aka aikata a cikinta har sai an barta.
Ga yadda maganar take
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
" من هوان الدنيا على الله أنه لا يعصى إلا فيها ، ولا ينال ما عنده إلا بتركها ."
FASSARA
-----------------
" Yana daga cikin qasqancin duniya a wajen Allah cewa shi ba a sabo (committing a sin) sai a cikinta , kuma ba a samun abinda ke wajen Sa (Allah) har sai an barta (duniya) ."
Ba za a taba samun sakamakon ayyukan bayi a cikinta ba domin ita ba gida ne na dawwama ba.
Saboda haka duk wani shege zai iya yin shegantakarsa, matsiyaci yayi tsiyarsa, azzalumi yayi zaluncinsa, munafuki yayi munafurcinsa, mahassadi yayi hassadarsa, makiri yayi makircinsa kuma fajiri yayi ta fajircinsa .
Amma da shike lahira ita ce gidan gaskiya na tabbata (DARUL-QARAAR) sai Allah ya girmamata ta yadda shege bai isa yin shegantaka a cikinta ba , kuma ta zama gurin yin hisabi don sakawa kowa gwargwadon aikinsa.
(THERE IS NO ANY NARROW ESCAPE AT THERE)
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
15th Sep, 2020/ 27th Muharram, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com