Matsalar Tsaro:- Yau kwana Goma Bansamu Runtsawa ba!!_ Cewar Wani Mai unguwa




Wani mai unguwa a garin kwanar farakwai yace yau kimanin kwanaki goma kenan bai samu damar barci ba sabida barazanar tsaro da suke fuskanta a yankin.

Ya bayyana haka ne a cikin jawabin godiya da ya gabatar ga yan uwa musulmi al-majiran Shaikh Ibrahim Zakzaky a wajen mu'utamar na kwana daya wadda da'irar Zariya ta shirya a garin na kwanar farakwai.

Mai unguwan ya nuna farin ciki tare da jin dadin sa game da yadda yan uwa suka bada gudunmuwar su wajen samar da tsaro ga jama'ar sa a lokacin gabatar wannan taron.

Ya kara da cewa yadda yaga an zagaye anguwannin garin da yan uwa harisawa ne, ya samar masa da kwanciyar hankali. "Yadda muka zagaya ta kowanne lungu muka ga yan uwa a ko'ina, sai na sami kwanciyar hankali" inji shi.

Daga karshe ya yi addu'ar allah karfafi yan uwa, sannan itama kwamitin tsaron garin ta nuna farin cikin ta game da tallafin da yan uwa suka basu, tare da addu'ar Allah ya karawa su Malam lafiya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post