Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato.
A wani bangare na jawabin da Sheikh Sidi Munir wakilin yan'uwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Alzakzaky na yankin Sakkwato ya gabatar a lokacin da yake mayar da martani ga takardar da Kwamishinan yan Sandan jahar Sakkwato Ibrahim Sani Ka'oje ya bayar ga manema labarai dangane da sintirin da jami'an tsaro ke yi a kwanukan da suka gabata a jahar ta Sakkwato. Inda a cikin takardar kwamishinan ya bayyana cewa, “sintirin da jami'an nasa ke yi a cikin gari suna yi ne domin kara inganta tsaro ba suna yi ne domin 'yan Shi'a ba.”
Sheikh Sidi Munir ya bayyana cewa, “wannan magana da Kwamishina ya yi, ya yi ta ne kawai domin Allah (T) hana su kaiwa ga mummunan kudurinsu, domin al'ummar garin Sakkwato baki dayansu, shaida ne akan cewa tun bayan fara zaman makokin Ashura da kwaki biyar jami'an tsaro suka fara shawagi a cikin gari, wanda kuma a karshe sukan je a muhallan yan'uwa su yi sansani, sa'annan kuma idan suka je sukan rika zage-zage ga yan'uwa tare da izgili kala-kala na yunkurin da suke dashi na zubar da jinanen bayin Allah. Al'ummar dake makwabtaka da Hussainiyya shaida ne akan wannan.”
Ya cigaba da cewa, “idan har dagaske Kwamishina ke yi, da wane laifi suke tsare da yan'uwanmu 6 da suka kama a bakin kofar Hussainiyya Imam Mahadi (ATF) dake unguwar Mabera da kuma makarantar Fudiyyah ? Yau Kusan kwanaki goma kenan ake rike dasu a ofishin na Kwamishina dake CID kuma har yanzu ba'a gurfanar dasu a gaban Kotu ba ba'a fadi laifinsu ba, haka kuma daga cikinsu akwai har wadanda kananun yara ne da basu isa ace an tsaresu ba.”
Ya kara da cewa, “lalle wannan magana ta Kwamishina ba gaskiya bace, duk abubuwan da suke yi suna yi ne domin hana yan'uwa zaman makokin Ashura da kuma muzaharar Ashura dalili akan haka kuwa shine, tun bayan da aka kammala zaman makoki aka kuma yi muzaharar Ashura, jami'ansa suka daina sintirin kamar yadda suke yi a lokacin da ake zaman makokin, ya dai yi wannan maganar ne kawai domin sun rasa abinda zasu gayawa jama'a na ganin duk iya kokarinsu basu iya hana yan'uwa yin muzaharar Ashura a Sakkwato din ba.”
A karshe Sheikh Sidi Munir ya yi kira ga Kwamishinan cewa, “idan dagaske ku ke yi tsaro ku ke son ingantawa a jahar Sakkwato, to mu ga Kwamishina da rudunar jami'ansa a garuruwan Sabon Birni, Isa, Gwaranyo, domin a can ne babu tsaro, a can ne barayi da yan bindiga ke cin karensu ba babbaka ba cikin gari ba, haka kuma ko a cikin garin akwai guraren da ake aikata ayukkan assha da dama amma ba a ga jami'an tsaro na sintiri a can domin hanawa.” 02/09/2020.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com