YANA DA KYAU YAN UWA MU FAHIMCI WANNAN!.......
A lokuta da dama nakan zauna nayi tunani sannan na tambayi Kai na 'shin menene dalilin da yasa wasu daga cikin al-ummar da muke zaune a cikin ta suka gaza fahimtar hakikanin kiran da Sayyid Zakzaky (H) keyi? , meya dalilin da yasa wasu suke jifan jagoran mu da kalaman da basu dace ba? Sannan kuma meya hujjar su akan Hadafin?.
Sau da yawa amsar da nake samu a cikin wadannan tambayoyin nawa shine 'Dabi'un mu', halayen da muke nuna wa a tsakanin al-ummun da muke rayuwa a cikin su, su sukafi jawo rashin fahimtar kiran da Sayyid Zakzaky ke yi a cikin al-ummar mu.
Sayyid Zakzaky bawan Allah ne wanda yake kira izuwa komawa ga aiki da Shari'ar Allah (T), wanda hatta masu yakar sa sun tabbatar da hakan. Sannan Sayyid (H) mutum ne wanda hatta makiyan sa ma sun sallama sa wajen kyawawan dabi'u, da yin uzuri ga kowa, amma abin takaici shine yadda wasu daga cikin yan uwa suka gaza zama masu koyi da Sayyid Zakzaky a aikace.
Malam Zakzaky yana cewa : "idan dabi'un yan uwa suka zamto irin ta yan Najeriya, to babu ranar sauyi", sai gashi abin takaici wasu daga cikin yan uwan sun dauki dibi'ar najeriyanci sun dabbaka a rayuwar su.
A ra'ayina idan har za'a afka mana sannan a kashe mu yan Najeriya suyi murna, mu bai kamata idan wani abu mara kyau ya sami daya daga cikin masu cutar damu mufito muna irin halayyar najeriyanci ba.
Babban misali ne ga yan uwa bayan kisan kiyashin da aka mana a zariya, duk da abin da mutane sukayi musamman ma mutanen gyallesu na murna da izgilanci, amma Sayyid Zakzaky yace a basu tallafin da ya saba bayar wa gare su. Wannan babbar misali ce sannan kuma abin koyi ga yan uwa. Mutum ko ya cutar da kai a matsayin ka mai da'awa bai kamata kaima ka zama macuci ba.
Ko ba komi Sayyid Zakzaky yana fadin cewa mu zamto jakadu na kwarai ga harka islamiyya a duk inda mu sami kan mu, a gaskiya abin da wasu yan uwa suka yi daga jiya zuwa yau akan rayuwar sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris, ba komai bane illa saddu ga wannan harkar. Kuma wani abu ne da mutane zasu dauka abin da harkar musulumci ke koyarwa kenan.
Allah ya ganar da mu ikon sauke dukkan hakkokin jagora.
___Ismail Nuhu___
21-09-2020