Makaranta: Haqqin Malami Akan Dalibin Sa!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


DAGA WA'AZOZIN IMAM ALI (A. S) 


Dangane da haqqin malami akan dalibinsa, Imam Ali (A. S) na cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


قال علي رضي الله عنه: " من حق العالم عليك إذا أتيته أن تسلم عليه خاصة، وعلى القوم عامة، وتجلس قدامه، ولا تشير بيدك، ولا تغمز بع DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

ينك، ولا تقول: قال فلان خلاف قولك، ولا تأخذ بثوبه، ولا تلح عليه في السؤال، فإنما هو بمنزلة النخلة المرطبة، التي لا يزال يسقط عليك منها شيء. ."


                 FASSARA 

                -----------------


" YANA DAGA CIKIN HAQQIN MALAMI A KANKA IDAN KAJE WAJENSA KAYI MASA SALLAMA TASA TA KANSA (khas), DA KUMA TA JAMA'AH BAKI 'DAYA , KA ZAUNA A GABANSA KUMA KADA KAYI NUNI DA HANNU SANNAN KADA KA RINTSE IDANUWANKA, KUMA KADA KACE, " WANE BA HAKA YA FADA MIN BA ."


KUMA KADA KAYI RIQO DA TUFAFINSA SANNAN DAKA KAJI KUNYAR WAJEN YIN TAMBAYA GARE SHI. DOMIN SHI (malamin) TAMKAR BISHIYAR 🌲 DIBINO CE MAI 'YA'YA WACCE BA ZA GUSHE BA TANA ZUBO DA WANI ABU GARE KA ."


(Mawa'izatul-Sahabah) 


                SHARHI 

              ---------------


Abin nufi da yi masa sallama (khas) shine kada ya zamana don kayi sallama ga jama'ar da ka tarar suna tare kace ba za kayi masa tasa sallamar ba, kamar dai yadda ake gaida malami ne ta musamman yayin da yazo muku wani programme. 


Ba ladabi bane ya zama don kaji abinda ya fada ya sha bamban da abinda wani malami ya fada ka nuna tamkar shi ba daidai ya fada maka ba .


Ta hanyar yin tambayoyi cikin hikima za ka sami ilimin abubuwa da dama wadanda ba ka sansu ba, kuma ko da kuskuren magana yayi zai iya ganewa ya gyara. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

        (08137925034)


21st Sep, 2020/ 4th Safar, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post