Maganar Duk Abinda Ke Cikin Sahihul Bukhari Ya Inganta, Zancen Banza Ne...!!



Agaskiyar Magana baduk abinda bukhari ya kawo acikin wannan littafin bane ya inganta domi  kuwa indai hakan ta tabbata to shi kanshi Addinin ya rushe.

Dalili kuwa shine sauda yawa acikin wannan littafin zakaga abu ya sãba da alqur'ani, ya sãba da wãqi'i sannan kuma ya sãba da hankali.

Abin Lura Anan shine : Shin Tayaya za'ace Maganar manzon Allah ta sãba da ta Allah? Idan kuwa ta sãbadin to wacce za'a dauka aciki? Maganar Allah Za"a dauka Koko ta Annabi?

Sannan idan bukhari ya kawo hadisin daya sãba da wãqi'i ya zamuyi kenan da ita?
MISALI : Bukhari Yace Idan Yaro yayi tsawon rai bazai stufa tukufba har sai alqiyamah tãtashi, To abin luta Anan shine : Shidai wannan Yaro tuntuni ya tsufa kai yama mutu tun shekaru samada dubu da dari biyu, to shikenan sai yazama kenan Annabi ya fadi abinda ba Gaskiyaba kenan? Subhanallah! Wannan bazai yiwuba.

Sannan idan bukhari ya kawo hadisi sai kuma sãba da hankali to ya zãmuyi da shi? Shikenan sai mu zama mahaukata kenan?

Gaskiya adai sãke tunani amma maganar duk abinda ke cikin SAHIHUL BUKHARI Ya inganta wannan zance banzane.

Allah ya bamu ikon ganin gaskiya da kuma karbarta alfarmar MANZON ALLAH(SAWA)...

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post