Ku Kasance Masu Jin Kunya Kamar Sahabi Abubakar Bn Quhafata !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KO KASHI ZAI YI YAKAN JI KUNYAR UBANGIJI


Jin kunya na daga cikin imani kamar yadda ya tabbata cikin hadisi Ma'aiki (S. A. W. W) , amma a wannan zamani rashin jin kunya ya zama tamkar abinda ke alamta wayewa ga mutum. Wanda ke jin kunya akan dauke shi ne a Matsayin bagidaje marar wayewa. 


Abubakar Sahabin Manzon Allah (S. A. W. W) ya kasance matsananci wajen jin kunyar Ubangijinsa ko da kuwa yayi biyan buqatarsa ce irin ta 'yan adamtaka. 


Ga riwayar da aka samo daga gare shi. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


قال أبو بكر رضي الله عنه: يا معشر المسلمين، استحيوا من الله عز وجل، فوالذي نفسي بيده، إني لأظل حين أذهب إلى الغائط في الفضاء متقنعًا بثوبي استحياء من ربي عز وجل. 



" YAA KU TARON MUSULMI ! KU JI KUNYAR UBANGIJI MAI GIRMA DA 'DAUKAKA , NA RANTSE DA WANDA RAINA KE HANNUNSA, LALLE NI NAKAN QASQANTA YAYIN DA ZAN TAFI YIN KASHI A MAKEWAYI INA RIRRIQE TUFAFINA SABODA JIN KUNYAR UBANGIJINA MAI GIRMA DA 'DAUKAKA !"


  (Mawa'izus-Sahaba) 


           ABIN LURA 

          -------------------


Kowa ya san yin kashi halal ne wanda babu zargi cikinsa balle zunubi, amma shi ya kasance yakan ji kunyar Ubangiji yayin da ya tashi don biyan wannan buqata. 


To, me yasa ku ba za kaji kunyar Ubangiji ba yayin da kuma tashi aikata abinda ya haneku aikatawa ?


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

          08137925034


22nd Sep, 2020/ 5th Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post