@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DARASI DAGA WAQI'AR KARBALA
Ita kalmar tawaye na nufin sabawa wani tsari ko karya wata qa'ida wacce wasu suka ginata kuma suka doru a kanta, sannan suke so kowa yayi biyayya da ita.
Duk wani tsari wanda aka ce hukuma ce ta tsara shi sannan kace ba za kayi biyayya ga wannan tsari ba saboda wata hujja qwaqqwara da ka dogara da ita, to, kai dan tawaye ne .
Wannan dalili yasa nace kowanne Manzo dan tawaye ne a zamaninsa, kuma mahukuntan wancan zamani na hukunta su ne da hukuncin 'yan tawaye.
Annabi Ibrahim (A.S) ma da kansa ya ambaci kansa da suna dan tawaye inda yake cewa;
" ....... LALLE NI 'DAN TAWAYE (barranta) NE DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA. "
(Zukhruf, aya ta 26)
kuma ko lokacin da Allah ya aiko da Manzonsa (S. A. W. W) abinda yace ya fadawa kafirar hukumar Makkah shine;
" KACE, YAA KU KAFIRAI ! NI BA ZAN BAUTAWA ABINDA KUKE BAUTAWA BA !"
(Suratul-kafiruun, aya ta 1-2)
Bisa wannan dalili yasa suke kiransa dan tawayen addini, domin ya shelanta musu cewa shi ba zaiyi biyayya gare su wajen bautar wanin Allah ba.
Imam Hussaini (A. S) ya zama babban samfuri wanda ya dabbaqa sunnar kakanninsa (A. S) kuma ya zama babban abin koyi gare mu.
Da ace ya miqa wuya ga Yazeed (L. A) to da ba ayi waqi'ar Karbala ba, kuma da babu qanshin ruhin muslimci zuwa wannan lokaci/zamani.
Koyi da Imam Hussaini (A. S ) da sahabbansa (R. A) shine tsirar mu duniya da lahira .
Yaa Allah ka qwato mana jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) tare da ba shi kariya da kuma tabbatar damu a qarqashinsa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Saturday 5th sep, 2020/ 17th Muharram, 1442
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com