-Sheikh Ibraheem Zakzaky (H).
"Sakon da muke cewa shi ne ya kamata kowannenmu ya ga zai sadaukar? Wannan ninancin ya bar mu. Kowannennmu ya yi tunanin wace gudummawa zai bayar wajen ceton al'umma? Kuma ya bayar da gwargwadon abin da zai bayar. Insha Allahu wannan al'umma ba za ta ci gaba da zama a yadda take ba. Amma zan yi muku wani albishir.
" Insha Allahu ko mutum ya sadaukar, ko ma kada ya sadaukar, wannan al'umma ba za ta ci gaba da zama a yadda take ba. Wasu za su sadaukar, sai dai a yi ba ka. Wato sai ya zama an yi, amma kai ba gudummawarka. Amma dai za a yi. Don in ba mu yi ba, wasu za su yi. Wasun nan ko su zama 'yq'yanmu ko wasu mutane.".
"Amma wani abu guda, very clear' shi ne ba mutanen wasu kasa ne za su zo su yi mana ba. Ba kuma Mala'iku ne za su sauko daga sama su zo su yi mana ba, ba kuma Aljanu ne za su yi mana ba. Ba sa rai a kan cewa wai mafitarmu daga waje ne, sam! Ba wata kasar da za ta zo ta cece ku, kune masu sadaukarwa ku fid da kanku."
"Amma insha Allahul azim da yardar Allah za a samu sauyi a wannan al'umma, ba za mu zauna a cikin halin da muke ciki ba. Kuma muna fatan Allah ya sa wannan ya zama da gaggawa. Kuma muna rokon sa ya sa mu a cikin jimlar wadanda za a yi amfani da su wajen kawo wannan sauyi."
Wani bangare na Jawabin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da ya gabatar bayan liyafar cin abincin babbar Sallah a shekarar 2014 a Hussainiyyah Bakiyyatullah Zariya.
-Sani Hamisu.