Tare da Hadiminku: Saifullah Ningi
RAYUWAR IYALI:
Aure alaka ce mai karfi tsakanin jinsin namiji da mace, kuma tsari ne da rayuwar dan'adam ta ginu a kansa, babu bambanci tsakanin mutumin zamanin farko da na wannan zamanin, ko mutumin gabas da na yamma. Addinin Allah tun daga annabawan farko har na karshe sun ba wannan lamarin muhimmanci, sun shata wa kowane jinsi iyakokinsa bisa tsari mai kayatarwa da zai kai ga tausayi da jin kai da taimakekeniya tsakanin wannan jinsin guda biyu domin samun alakar halas da ci gaban samuwar dan'adam.
*MATAKIN FARKO*
Tun farko idan za a farar da alaka tsanin namiji da mace a matakin farko ana sanya hankali ne domin rayuwa ta yi karfi da inganci, amma bayan an shiga fagen rayuwar tare wato bayan aure, to a lokacin kuma ana son yin alakar soyayya ne. Don haka wadanda suke fara rayuwarsu da soyayya suka yi wurgi da hankali to ba zasu ji dadin rayuwarsu ba lokacin da suka shiga fagen rayuwar aure, don haka hankali ne matakin farko sai soyayya ta biyo baya. Masu juya lamarin su fara da soyayya sannan kuma daga baya su ce zasu sanya hankali a rayuwarsu zasu samu cewa lokaci ya kure masu ba zasu iya ba. Wannan ne ake nufi da cewar *masu fara rayuwa bisa dogaro da hankali to zasu iya ci gaba da rayuwa bisa soyayya, amma wadanda suke fara rayuwa bisa soyayya to ba zasu iya ci gaba da rayuwa bisa hankali ba.*
Idan rayuwar ma'aurata ta fara da tsari da hankali da tunani mai kyau to zata kai su ga cin nasara da samun nutsuwar rayuwa, al'ummar da ta doru kan wannan tunanin zata samu rayuwar iyalinta cikin annashuwa da nutsuwar rai da jin dadin rayuwar tare. Al'ummar kuwa da ta saba wa wannan lamarin zata fuskanci rayuwa mai dacin gaske. Kuma wani abu shine, tun da tsarin nan yana bukatar wanda ba shi da wata maslaha a cikinsa kuma ya san halittar mutum da bukatunsa, don haka da bukatar koma wa mahaliccin mutum don sanin takamaimai me ya dace da shi da rayuwarsa a daidakunsa ko a al'ummance. Wannan lamarin ne ya sanya muke jin kiraye-kiraye a kasashen yammacin duniya kan a koma wa addinan Allah cikin abin da ya shafi tsarin rayuwar iyali don samun nutsuwa da daidaito a ciki.
Zamu ci gaba insha Allah
✍️ *Saifullah Ningi*