Abbagano✍
Babu wata rayuwa mai muni kamar rayuwar Gizo-Gizo,
Gizo-Gizo suna haɗu wa ne dashi da matar sa don su gina gidan da zasu zauna domin rayuwa
Saidai idan macen taɗau ciki harta fara yin ƙwai, to daganan ne namijin zai koma neman abinda za su ci shi shi kaɗai.
Bayan ta kusa ƙyanƙyashe ƴaƴan ta, to zata fara tunanin gidan bazai ishe su zama ba, ita da mijinta ga kuma ƴaƴan dazata ƙinƙisa, daganan sai ta kashe mijin ta, ta rataye shi waje.
Bayan ta ƙinƙishe ƴaƴanta ta ciyar dasu har zuwa lokacin dasuka fara wayo, to daga nan suma sai su fara tunanin gidan bazai ɗauke suba su da uwar tasu,
Don haka sai su kashe ta su rataye ta, ko su cinye ta.
Suma daga nan kowa zai kama gaban sa don gina rayuwar sa, a irin wannan yanayin!!!
A bisa hakan ne Allah ya saukar da faɗin sa
وَإِنَّ أَوْهَنَ الْبُيُوتِ لَبَيْتُ الْعَنكَبُوتِ ۖ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ )
العنكبوت (41) Al-Ankaboot
(lalle mafi raunin gidaje, shi ne gidan gizogizo, da sun kasance suna sane.)
KUNSAN YANDA WASU TURAWA SUKE RAYUWAR SU SUMA?
Mutum zai dage ya nemi kuɗi dan gina gidan sa, ya kuma sha wahala don yin aure, har yakai ga yasamu ƴaƴa.
Bayan ya tsufa sai waɗan nan yaran daya sha wahalar kula dasu tun suna yara ya sanya su makaranta yayi musu duk abinda uba kewa ƴaƴa, Amman a haka zasu ce ya tsufa zaman sa a gida bazai yiwu ba
Sai su ɗauke shi su kai shi gidan kula da tsofaffi, a can zai ƙare rayuwar sa, arhali ga gidan daya gina na da kuɗin sa an fidda shi daga cikinsu ciki
Rayuwar waɗan nan mutane tayi kama da rayuwar Gizo-Gizo.
Mene ne ya sabbaba musu hakan ?
( مَثَلُ الَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ أَوْلِيَاءَ كَمَثَلِ الْعَنكَبُوتِ اتَّخَذَتْ بَيْتًا ۖ
Misãlin waɗanda suka riƙi waɗansu masõya waɗanda bã Allah ba, kamar misãlin gizõgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhãli kuwa
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com