Ko Kun San:- Shekaru 22 da afkuwar wakiar kutama


WAIWAYE ADON TAFIYA


A yau shekaru 22 da afkuwar wakiar kutama

Da sunan Allah mai turmuza hancin azzalumai, mai taimakon wadanda aka zalunta. Tsira da aminci su kara tabbata ga shugaban shiriya taskar ilimin Allah Muhammad dan Abdullahi da iyalan gidansa masu tsarki, wadanda suka kasance jirgin Nuhu ga wannan al'umma musamman Abu Abdullahi Hussain dan Ali wanda sakamakon jajensa ne wannan waki'a ta afku.

Wannan waki'a ta faru ranar 15 ga Muharram 1420 daidai da 30 ga Afrilu 1999 sa'ilin da akaje tunatarwa a wannan gari na Kutama.

Gamayyar yan tauri kimanin dubu daya ne suka afkawa Yan uwa da sara da duka da gorori, da adduna, takubba da nau'in makamai iri-iri.

Kafin faruwar hakan yan taurin garin sun shahadantar da dan uwa Shahid Ibrahim Bala ranar 13 ga Muharram, ta hanyar yi masa yankan Rago kamar yadda akayiwa Imam Hussain (AS). Kusan shine shahidin farko da akayiwa yankan Rago a tarihin wannan harka. wannan yasa Yan uwa daga Kano sukaje mota 2 domin haduwa da yanuwa na kutama a gabatar da tunatarwa, sai ya zama tun a kofar gari yan taurin sun tari yan uwa suka afkar da wannan waki'a.

Gasunayan Shaheedan da akasamu a irin wannan ranaku tsakanin 13 ga muharram Zuwa 15


*1.Shaheed Ibrahim guruzawa*

*2.Shaheed Saminu Shanono*

*3.Shaheed Yahaiya Badawa ta kano*


Wadannan sune shahidan da akasamu a waki'ar garin kutama

Daga waki'a taci gaba alokacin.
Kuma submaharan sun sami hadin kan wasu Malamai da Masugari musamman Hakimin Gwarzo Sa'ad Bayero. Dama al'amarin harkar ya dame su, yadda suka ga Da'awar Malam Zakzaky (H) tana ta yauwa da bunkasa a garin.

A wannan waki'a lallai Yan uwa Mata sunsha wahala ta yadda aka rika dukansu da kona musu hijabai ciki har da Mahaifiyata, ta labarta min irin wahala da tasku da suka sami kansu a wannan lokacin, ga su kuma iyayen mu maza da sauran yanuwa an gudu cikin daji domin tsira da rai (ita muke kira hijirar daji). Ga zagi da cin mutuncin na fitar arziki da kafirtawa, yawo da yawatawa yai wahala ga almajirin Sayyid Zakzaky (H).

 A irin labarin da Mahaifiyata ta bani na irin yanayin da ta sami kanta take cemin "Sun bugeni sosai suka konan Hijabi suka kwashemin kayan dakina kaf, suka doki abokiyar zamana suka hadata da kyauren kofa a take tayi bari".

Sun kama yan uwa da dama har takai da ankai su kurkuku, ga masu munanan raunuka. Duk juma'a sai an tura jami'an tsaro sun tsaya akan al'umma lokacin da ake sallar juma'a.

*TO YANZU GA HARKA KARKASHIN JAGORANCIN ALLAMA SAYYID ZAKZAKY A KUTAMA*

Yanzu ga yan uwa a kutama, in ka gansu saikai mamaki kuma kullun karuwa muke, muna fa Fudiyya nuna komai na harka, alhamdulillah.

Yau gashi masu mulkin mafi yawa ba mukamin, Yan siyasar ba mulkin irin su Kwankwaso, Yan Taurin wasu ciwon ido ya kashe su, wasu ciwon hannu kusan mafiya yawa sun bar duniyar cikin kaskanci da wulakncin rayuwa, wasu kuma harkar ta mamayi 'yayansu dasu ake yi.

Allah muna gode ma, ka kara mana juriya da sabaty. Ya Allah ka kwato mana Jagoranmu Allama Sayyid Zakzaky (H) cikin izza da karama ka ba Sayyid lafiya da mai dakinsa da dukkan Yan uwan da basu da lafiya.

Muna kara nanatawa da Babbar murya.

LABBAIKA YA HUSSAIN

*LABBAIKA YA AL-ZAKZAKY*

_Hussaini Tasiu Kutama_

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post