MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
DAGA BAKIN IMAM ALI (A. S)
Nau'in masharranta na da yawa domin za ka ji ana ambatonsu a gurare da dama, amma mun so yin amfani da wannan hadisin da yazo daga Imam Ali (A. S) don ganin yadda yawancin mutane suka kasance a wannan zamani.
Mafi yawan mutane sun shagaltu ne da ganin aibobin wasu maimakon kallon kansu ko su gyara.
Irin wadannan sun fi sharri cikin al'umma don su suke yada/haddasa fitintinu masu wuyar shawo kansu. Saboda haka akwai buqatar a nesance su.
Ga dai hadisin nan kamar haka,
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
" MAFI SHARRIN MUTANE SHINE WANDA YA KASANCE YANA BIBIYAR AIBOBIN MUTANE KUMA YA MAKANCE DAGA KALLON NASA AIBOBIN. "
(taraa'iful-Hikaam, shafi na 176)
Za ka sami irin wadannan mutane a kullum suna qoqarin gamsar da mutane su fahinci haqiqanin aibun wani don wata manufa irin tasu da ke qunshe cikin zuciyarsu.
Allah ya tsare mu daga sharrukansu, ya kuma shagaltar damu bisa kallon aibobinmu mamakon na wasunmu
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda
09039791509
2nd September, 2020- 14-2-1442
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Tags:
Tunatarwa