SHEKARU 60 DA KARBAR SUNAN 'YANCI
Nijeriya kasa ce da yan cikinta suke tutiyan sun samu yanci daga mulkin mallakar Turawa da suka yi na tsawon lokaci bayan rushe daular Muslunci wanda Mujaddadi Shehu Usman Danfodio ya kafa a Shekarar, bayan sun kashe Sarakunan Musulmi tare da kona tutar Muslunci a wancan lokacin. A yau Alhamis ne Yan kasar suke bikin cika Shekaru 60 da sunan samun yancinsu, inda a gefe guda kuma zamu iya cewa ba a samu wannan yancin da ake fada ba.
Nijeriya kasace da har yanzu take karkashin mulkin turawan Ingila dama wasu manyan kasashen duniya duk da cewa an bayyana kasar ta samu yancinta tun shekarar alam 1960. Kasashen tutawa sun kasance sune suke cigaba da yiwa kasarmu Nijeriya Mulkin mallaka domin kuwa duk da bada yancin da suka yi a baki sune suke juya kasar.
A tarihin kasarmu Nijeriya ba a taba samun ba a taba samun Shugaban kasar da mu al'umman kasar ne muka zabe sa da kanmu ba face sai kasashen turawan duniya sun aminta dashi kuma ya yarda zai aiwatar musu da aikin da suke bukata, Kasashen turawa na cigaba da mulkar mu a yanzu domin su Shugabannin kasar Nijeriya suna karban umarni ne daga turawa idan kuma ka sabawa maganar su suna iya hallaka ka, Janaral Sani Abacha zai iya zama mana babban misali domin ya guje turawan dasu da umarninsu wannan yasa suyi amfani da mace wajen kashe shi. Turawan suna amfani da Shuwagabannin kasar da masu girma a kasar wajen cimma muradinsu na kwasar dukiyar kasarmu da duk wani abu mai amfani.
A wannan lokaci da ake bayyana kasar ta samu yanci, kasa she da take fama da tashin hankali kala daban-daban tun daga kan Boko Haram, Yan fashi, Masu sace Mutane (Kidnappers) barayin shanu, rikicin addini da kabila, da wasu nau'o'in ta'addancin kala daban-daban ciki kuwa har da mugun Talauci da yake addabar kasar. Kasa ce wanda ake iya kashe wanda aga dama a lokacin da ake so, a karya dokar da aga dama, kasa ce da a mayar da talakawan cikinta tamkar bayi.
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya kasance mai kira da a kawar da tsarin da turawan mulkin mallaka suka dora kasar a kai na mulkin Demokradiya mulki mai cike da rashin karrama da Adam, mulki mai cike da zakunci da danniya, domin komawa tsarin Allah (S) kaman yanda Shehu Usmanu yayi a shekarun da suka shude. Sheikh Zakzaky ya shafe Shekaru 40 yana wannan kiran, wanda hakan yasa tun farkon fara kiran nasa Masu mulkin kasar basu barshi ba saboda tsarin da yake kokarin kawowa ya saba daba iyayen gidansu, tsarin da zai kawo zai rushe duk wani mulki nasu su kuma turawan zai zama Nijeriya ta gagaresu a komai idan su bari Zakzaky ya tabbatar da wannan kiran. Wannan yasa a Shekaru 40 da ya kwashe yana wannan da'awar ake ta yunkurin kashe shi ta kowace hanya, wanda harin karshe da a kai masa shine wanda turawa su saka Gwamnatin Buhari ta kai masa a Shekarar 2015 har yanzu suna cigaba da tsare shi duk da wata babban kotun kasa dake Abuja ta bayyana a sake shi tun a Shekarar 2016.
- Ibrahim Almustapha Saminaka
- 1/October/202