Ko Kasan Wanda Yafi Kowa Daraja, Cikin Mutane: Amsa Daga Bakin Fiyayyen Halitta (s.a.w.w)


 

@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Fifiko ba a dukiya ko mulki ake samunsa ba, domin kowanne daga cikinsu yakan gushe. Kuma duk wani abu da zai iya gushewa daga wani ya koma kan wani bai zama abin fifiko ko alfahari ba. 


Domin sanin wanda yafi kowa daraja cikin mutane duba wannan hadisi 


👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽👎🏽



عَنِ الْمُفَضَّلِ عَنِ الصَّادِقِ ع أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ ص قَالَ: أَعْلَمُ النَّاسِ مَنْ جَمَعَ عِلْمَ النَّاسِ إِلَى عِلْمِهِ وَ 

أَكْثَرُ النَّاسِ قِيمَةً أَكْثَرُهُمْ عِلْماً وَ أَقَلُّ النَّاسِ قِيمَةً أَقَلُّهُمْ عِلْماً.

أقول: الخبر بتمامه في باب مواعظ الرسول ص


Abinda hadisin ke cewa shine; 


Daga Mufaddhal, daga Imam Sadiq (A. S), daga Annabi (S. A. W. W) yace; 


" MAFI ILIMI DAGA MUTANE SHINE WANDA YA TARA ILIMIN MUTANE ZUWA NASA (ilimin), KUMA WANDA YAFI MUTANE QIMA (daraja) SHINE WANDA YA FI SU ILIMI , KUMA QASQANCE CIKIN MUTANE SHINE WANDA YA FI SU QARANCIN ILIMI ."


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 164


               DARASI 

            ------------------


Darasin da ke cikin wannan hadisi shine, mu daga mu nemi ilimin kowanne fanni na addini ko zamani, kuma na kowacce mazhaba ko aqida. 


Sanin wannan ilimi shi zai fifita mu akan wasunmu, domin wanda ya fi ka sanin ilimin gidanka bayan sanin ilimin nasa gidan ya fi ka.


 Shi kuwa jahili shine qasqantacce cikin kowacce al'umma.


Da irin wannan fifiko Allah ya fifita Annabawa da A'imma (A. S), kuma ya fifita magadansu na wannan zamani akan sauran jama'a .


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


             08137925034


Monday 7th Sep, 2020/ 19th Muharram, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post