Karamar Sayyid Zakzaky (H) Irin Ta Annabi Ibrahim (A.S) Ce!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


NI'IMAR ALLAH YAYIN SAUKAR BALA'I 


Babu wani Annabi , Imami ko kuma wani mai tajdidi addinnin Allah ba tare da ya ci karo da zaluncin mahukuntan zamaninsa ba, sai dai Allah na taimakonsu a kansu ta kowacce fuska. 


Ya zo daga Abu Abdullahi (A. S) yana cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 وَ قَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع‏ لَمَّا أُجْلِسَ إِبْرَاهِيمُ فِي الْمَنْجَنِيقِ وَ أَرَادُوا 

أَنْ يَرْمُوا بِهِ فِي النَّارِ أَتَاهُ جَبْرَئِيلُ فَقَالَ السَّلَامُ عَلَيْكَ يَا إِبْرَاهِيمُ وَ رَحْمَةُ اللَّهِ وَ بَرَكَاتُهُ أَ لَكَ حَاجَةٌ فَقَالَ أَمَّا إِلَيْكَ فَلَا فَلَمَّا طَرَحُوهُ دَعَا اللَّهَ فَقَالَ يَا اللَّهُ يَا وَاحِدُ يَا أَحَدُ يَا صَمَدُ يَا مَنْ‏ لَمْ يَلِدْ وَ 

لَمْ يُولَدْ وَ لَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُواً أَحَدٌ فَحُسِرَتِ النَّارُ عَنْهُ وَ إِنَّهُ لمحتبى‏[20] [لَمُحْتَبٍ‏] وَ مَعَهُ جَبْرَئِيلُ وَ هُمَا يَتَحَدَّثَانِ فِي رَوْضَةٍ خَضْرَاءَ.


" Yayin da aka ajiye Ibrahim (A. S) cikin majajjawa akayi nufin jefa shi cikin wuta sai Jibrilu yazo masa yace; 


AMINCIN ALLAH DA RAHMARSA DA ALBARKARSA SU TABBATA A GARE KA YAA IBRAHIM , SHIN, KANA DA WATA BUQATA NE? yace, 


" KAIMA HAKA GARE KA. A'A, (ba ni da wata buqata a wajenka sai taimakon Allah). "


A lokacin da aka jefa shi (cikin wutar) sai ya kirayi Allah yace, 


" YAA ALLAHU, YAA TILO , YAA MAKADAICI, YAA WANDA AKE NUFI DA BUQATA, YAA WANDA BAI HAIFA BA KUMA BA A HAIFE SHI BA, KUMA (wanda) BABU TAMKA A GARE SHI !"


Sai aka kwaranyar da wutar daga gare shi yana wanda aka tsare, kuma Jibrilu na tare da shi suna hirar su a wani lambu kore. "



وَ رَوَى الْوَاحِدِيُّ بِإِسْنَادِهِ إِلَى أَنَسٍ عَنِ النَّبِيِّ ص قَالَ: إِنَّ نُمْرُودَ الْجَبَّارَ لَمَّا أَلْقَى إِبْرَاهِيمَ فِي النَّارِ نَزَلَ إِلَيْهِ 

جَبْرَئِيلُ بِقَمِيصٍ مِنَ الْجَنَّةِ وَ طِنْفِسَةٍ مِنَ الْجَنَّةِ فَأَلْبَسَهُ الْقَمِيصَ وَ أَقْعَدَهُ عَلَى الطِّنْفِسَةِ وَ قَعَدَ مَعَهُ يُحَدِّثُهُ.



Annabi (S. A. W. W) yace; 


" LALLE YAYIN DA NAMARUDU JABBERI YA JEFA IBRAHIM CIKIN WUTA SAI JIBRILU YA SAUKO ZUWA GARE SHI DA WATA RIGA DAGA ALJANNAH DA WATA SHIMFIDAR ALJANNAH. YA SANYA MASA RIGAR KUMA YA ZAUNAR DA SHI KAN WANNAN SHIMFIDA , SHIMA YA ZAUNA TARE DA SHI SUNA HIRA (don debe masa kuwa). "



و قال كعب ما أحرقت النار


Ka'ab yace, wuta bata qona shi ba. 

__________________________

(1) مفاتيح الغيب 6: 131- 132. م.


(2) حسرت عنه أي انكشفت عنه. احتبى بالثوب: اشتمل به. جمع بين ظهره و ساقيه بعمامة و نحوها. و في المصدر: و إنّه لمحتب.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏12، ص: 25


Irin wannan kariya Allah ya bawa Sayyid Zakzaky (H) ko da kuwa wasu basu sani ba. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

        (01826385470)


20th Sep, 2020/ 3rd Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post